Lai Mohammed ya fadi abin da ya sa Buhari ya gagara shawo kan abubuwa cikin shekara 7

Lai Mohammed ya fadi abin da ya sa Buhari ya gagara shawo kan abubuwa cikin shekara 7

  • Ministan yada labarai da al’adun kasa ya kare gwamnatin Muhammadu Buhari daga masu suka
  • Alhaji Lai Mohammed ya ce har yanzu ana ta kokarin gyara barnar da 'Yan PDP suka yi a baya ne
  • Mohammed ya ce Buhari na bakin kokarinsa, kuma bai dace PDP ta rika sukar gwamnatinsa ba

Abuja - Ministan yada labarai da al’adun kasa, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana abin da ya jawo gwamnatin APC ta gaza shawo kan wasu matsalolin Najeriya.

Kamar yadda Legit.ng ta samu labari, Lai Mohammed ya yi wannan bayani a lokacin da ya yi magana da ‘yan jarida a ranar Litinin, 28 ga watan Maris 2022.

Ministan labarai da al’adun ya ce har yanzu gwamnatin tarayya ta na fama da wasu daga cikin matsalolin da ta gada daga wajen gwamnatin PDP ne tun 2015.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Ba Najeriya kadai ke fama da tsadar kayan abinci da man fetur ba

Lai ya fadawa manema labarai cewa don haka, jam’iyyar hamayya ta PDP ba ta da hurumin da za ta fito, ta na sukar APC da ta ke yin iya bakin kokarinta a yau.

Shekaru 4 sun yi kadan - Lai

Mohammed ya ce jam’iyyar PDP ce ta kashe Najeriya a tsawon shekaru 16 da tayi a kan mulki. Ministan ya ce shekaru hudu ba za su isa a gama gyaran ba.

This Day ta ji Ministan ya na cewa sukar da PDP ta ke yi wa gwamnatin APC tamkar mai amalala ne yake dariya ga mai wanke gadon da ya yi wa sharkaf da fitsari.

Lai Mohammed
Alhaji Lai Mohammed a ofis Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Najeriya na shigo da fetur har gobe

Har yanzu Ministan ya na bada uzuri, ya ce gwamnatocin PDP sun amfana lokacin da fetur ya yi tsada a Duniya, amma ba su iya gyara matatun da ake da su ba.

Kara karanta wannan

Hotunan Abba Kyari a gaban kotu: Kotu ta ki amincewa da ba da belin DCP Abba Kyari

Alhaji Mohammed ya ce a shekarar nan za a bude matatar Dangote, wanda a cewarsa hakan ya nuna yadda gwamnatin Buhari ta ke taimakawa ‘yan kasuwa.

“Gwamnatin PDP ba ta iya gyara matatu ba. Abin da ke faruwa a yau shi ne har yau mu na shigo da mai ne.
“Gwamnatin nan ta kaddamar da karamin matata daya, kuma akwai kananan matatu uku da suke nan tafe.”
“Kamar mutum ne ya yi shekaru 16 ya na barna, kuma ana fatan mu gyara ta’adinsu a cikin shekaru hudu.” - Lai

Ka da mutane su zabi PDP a 2023

Har ila yau, Ministan ya yi kira ga jama’a da cewa ka da su biyewa yaudarar PDP a zaben 2023, domin mai garkuwa da mutane ba zai taba zama mai ceto mutum ba.

Daga cikin nasarorin da aka samu a gwamnatin nan a cewar Ministan, Najeriya ta na fita da kayan abinci zuwa kasashen makwabta, ta na ciyar da mutanen Afrika.

Kara karanta wannan

Abin da wasu wadanda suka yi takara a APC suke fada, bayan sun sha kashi a zaben kasa

Mulki ya zo karshe

A makon nan aka tuna maku cewa nan da watanni biyu za ayi zaben fitar da gwani a APC mai mulki, irindu Bola Tinubu da abokan gabansa za su san matsayarsu.

Babu mamaki ‘Dan siyasar da zai nemi mulki a karkashin APC bayan Muhammadu Buhari ya ba jama'a mamaki domin akwai yiwuwar a dauko wani bare daga gefe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel