Gwamnatin Buhari: Ba Najeriya kadai ke fama da tsadar kayan abinci da man fetur ba

Gwamnatin Buhari: Ba Najeriya kadai ke fama da tsadar kayan abinci da man fetur ba

  • Gwamnatin tarayya tace ba a Najeriya kadai ake tsadar kayan abinci da man fetur ba
  • Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya ce masu adawa ne ke kulla-kulla tare da nuna abun kamar iya Najeriya ne
  • Ya ce gwamnatin Buhari ta samu gagarumin nasarori a dukkan bangarori, duk da matsalolin da kasar ke fuskanta

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce karin da aka samu a farashin wasu kayan abinci, fetur, diesel da sauran kayayyaki abune da ake fama da shi a duniya gabaki daya, ba wai iya wata kasa bace.

Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, ya kara da cewar gabatar da lamarin a matsayin matsalar Najeriya makirci ne, rashin gaskiya da kuma batarwa, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yakin Rasha Da Ukraine Na Iya Tsananta Talauci a Najeriya, Oxfam Ta Yi Gargadi

Gwamnatin Buhari: Ba Najeriya kadai ke fama da tsadar kayan abinci da man fetur ba
Gwamnatin Buhari: Ba Najeriya kadai ke fama da tsadar kayan abinci da man fetur ba Hoto: guardian.ng
Asali: UGC
“Wannan kididdiga da ake amfani da shi makirci ne karara. Wadanda ke yayata wannan alkaluman ba tare da daura su a ma’auni ba rabin wayo ne da su.
“Mu duba farashin kayan abinci da fetur. Ku duba farashin kayan abinci a sauran kasashe, musamman UK da US ta Google, za ku ga cewa sun tashi.”

Ministan ya kara da cewar karancin man fetur da aka samu a fadin kasar a kwanan nan ya fara yin sauki, yayin da matakan da gwamnati ta dauka ya fara aiki.

Ya jadadda cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu gagarumin nasarori a dukkan bangarori, duk da matsalolin da kasar ke fuskanta, rahoton Independent.

Mohammed ya bukaci yan Najeriya da su lura da karairayi da batarwar masu adawa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Hukuncin kotu kan dokar zabe ta Buhari ya raba kan Sanatoci

Ya kara da cewa:

“Yan Najeriya na cikin dimuwar mulkin zaluncinsu na shekaru 16, kuma ba za su koma ruwa ba ta hanyar barinsu su koma kujerar mulki.”

Najeriya na kara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali kullum, Gwamnatin Buhari

A wani labarin, Gwamnatin tarayya tace Najeriya na samun zaman lafiya da aminci kowace rana tare da nasarori a yaƙin da take da Boko Haram/ISWAP, yan bindiga da sauran ayyukan ta'addanci.

Ministan yaɗa labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ne ya faɗi haka a wurin taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Yace dakarun tsaro a Najeriya sun zafafa yaƙi da yan bindiga kuma suka jefa su cikin halin gudun ɓuya yayin da kullum ake ƙara tarwatsa sansanonin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel