Hotunan matashi mai hidimar kasa da ya rasu a sansanin NYSC na Kebbi

Hotunan matashi mai hidimar kasa da ya rasu a sansanin NYSC na Kebbi

  • Matashi mai hidimar kasa ya yanke jiki ya fadi a sansanin NYSC da ke Dakingari a jihar Kebbi inda ya rasu a take
  • Matashin mai suna Musa Momoh Tunde, ya kammala digirinsa daga foliteknic ta tarayya da ke Bida inda ya ke Kebbi domin hidimtawa kasa
  • Tuni aka yi janaizar Tunde kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar tare da birne shi, inda ya sha yabo kan kyawawan halayensa

Dakingari, Kebbi - Babban Darakta Janar na Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC), Manjo-Janar Shuaibu Ibrahim ya mika ta’aziyya ga iyalan wani matashi mai suna Musa Momoh Tunde, mai lambar hidimar kasa (KB/22A/2278) wanda ya rasu a sansanin wayar da kai na NYSC da ke Dakingari a Jihar Kebbi. .

Kara karanta wannan

Na yi mankas da kwayoyi kafin in zaneta: Matashin Bakano da ya halaka kakarsa, ya jefa gawarta a rijiya

Marigayi Tunde, wanda ya kammala digirinsa a fannin Hulda da Jama'a a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Bida, ya yanke jiki ya fadi inda ya rasu a yammacin ranar Juma'a, 26 ga watan Maris, a lokacin da yake kallon daya daga cikin wasannin kwallon kafa a sansanin NYSC.

Hotunan matashi mai hidimar kasa da ya rasu a sansanin NYSC na Kebbi
Hotunan matashi mai hidimar kasa da ya rasu a sansanin NYSC na Kebbi. Hoto daga Momoh Hans
Asali: Facebook

Darakta Janar na NYSC a sakon ta’aziyyarsa wanda Barista Ahmed Tijjani ya gabatar, ya bayyana dan bautar kasa Musa Momoh Tunde a matsayin matashin dan Najeriya mai kishin kasa wanda ya rasu yana yi wa kasa hidima.

Ya shawarci ‘yan uwansa da su rungumi mutuwarsa a matsayin wani iko na Allah tare da lura cewa babu makawa mutuwa ga kowa kuma tana iya zuwa lokacin da babu wanda ya yi tsammani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban ya ci gaba da cewa, marigayin ya rasu ne a matsayinsa na matashi mai martaba wanda kuma a shirye yake da kuma sha’awar bayar da gudummawar kasonsa ga ci gaban kasa kuma za a iya tunawa da shi a matsayin dan Najeriya mai son kasa da kishin kasa.

Kara karanta wannan

Kada ka yaudari Tinubu, idan ba haka ba karshenka ba zatayi kyau ba: Fasto ga Osinbajo

Malam Yahaya Mohammed, yayan marigayin wanda ya yi magana a madadin ‘yan uwansa, ya ce sun ji mutuwar ganin yadda marigayin ya yi rayuwa mai kyau kuma ya rasu cikin mutunci da kuma yi wa kasa hidima.

A halin yanzu, an yi jana’izar dan bautar kasan kuma an birne shi a makabartar jihar Kebbi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

A bidiyo mai taba zuciya, angon amaryar da aka birne ranar bikinsu yace ta ji a jikinta mutuwa za ta yi

A wani labari na daban, a ranar da ya kamata a yi shagalin bikinta, wata matashiyar budurwa 'yar shekara 22, mai suna Mutoni Uwase Kenia aka yi bikin birne gawarta.

An birneta a ranar Juma'a, 3 ga watan Maris, 2022. Kenia ta bukaci sake ma ta aiki don bude ma ta mahaifa, amma hakan bai yuwu ba, saboda ita da mijinta basu iya biyan kudin yin aikin.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya rafke matar aure da tabarya, ya halakata a gaban yaranta a Kano

Afrimax ne suka wallafa yadda Kenia ta hadu da Jack Jack da labarin soyayyar su a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel