Da duminsa: Yan takaran kujeran shugaban APC 6 sun janyewa wanda Buhari ya zaba, Abdullahi Adamu

Da duminsa: Yan takaran kujeran shugaban APC 6 sun janyewa wanda Buhari ya zaba, Abdullahi Adamu

  • Daga karshe, dukkan yan takara kujeran shugabancin uwar jam'iyyar APC mai mulki sun yi biyayya wa shugaba Buhari
  • Yan takara ranar Alhamis sun zanta da shugaban kasa a fadar Aso VIlla kan lamarin zaben sabon shugaba
  • Yan takaran gaba daya a wasikar da suka aikewa sakataren gwamnatin tarayya sun ce babu komai sun amince

Abuja - Yan takaran kujeran shugabancin jam'iyyar All Progressives Congress APC sun janye daga takarar kujeran wa abokinn takaransu, Sanata Abdullahi Adamu.

Abdullahi Adamu ne zabin Shugaba Muhammadu Buhari.

Yan takaran sun bayyana hakan a wasika mai ranar wata 25 ga Maris, 2022.

Wasikar wacce Ministan harkoki na musamman George Akume ya rattafa hannu madadin sauran yan takaran tace:

"Bisa rokon da Shugaban kasa yayi ga masu takaran kujerar shugabancin jam'iyyar su amincewa mutum daya, mun janyewa Sanata Abdullahi Adamu kuma mun yi ittifaki kansa kuma wadannan yan takara sun aika wasikunsu:

Kara karanta wannan

Maye: Abu 5 da ya kamata ku sani game da Abdullahi Adamu, mutumin da Buhari ya zaba matsayin shugaban APC

1.H.E Sen. Tanko Al-Makura

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. H.E Sen. George Akume

3. H.E Abdulaziz Yari

4. Sen. Sani Musa Muhammed

5. Comm. Etsu Muhammed

6. Turaki Saliu Mustapha.”

Buhari ya fadawa jam’iyyar APC ta maidawa duk wani ‘dan takara da ya hakura da neman mukami kudinsa

Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadawa jam’iyyar APC ta maidawa duk wani ‘dan takara da ya hakura da neman mukami kudinsa.

A ranar Laraba, 23 ga watan Maris 2022, Punch ta rahoto shugaban kasa yana umartar APC ta maidawa wadanda suka janye takara kudin fam da suka biya.

Wasu ‘yan siyasa sun fasa takara, sun yarda su janyewa abokan hamayyarsu. Don haka Muhammadu Buhari ya hana APC taba irin wadannan kudi.

Haka zalika, Mai girma Buhari ya fadawa gwamnonin jam’iyyarsa da su yi kokari wajen ganin an zabi sababbin shugabannin APC na kasa ta hanyar maslaha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel