'Karin Bayani: An Gano Ɗan Sheikh Pantami Da Masu Garkuwa Suka Sace

'Karin Bayani: An Gano Ɗan Sheikh Pantami Da Masu Garkuwa Suka Sace

  • An tsinci daya daga cikin 'ya'yan Farfesa Ali Isa Pantami, Al'amin Isa Ali Pantami a Dambam, Jihar Bauchi awanni bayan masu garkuwa sun sace shi
  • Majiyoyi sun tabbatar da afkuwar lamarin amma ba su bayyana ko an biya kudin fansa ba kafin sako shi, ko ba a biya ba
  • Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Bauchi, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ba a kai musu korafi kan lamarin ba

Jihar Bauchi - An ceto dan ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Ali Isa Pantami, da aka rahoto cewa an sace shi a jihar Bauchi, Daily Trust ta rahoto.

A cewar majiyoyi, an gano dan ministan ne a Dambam, daya daga cikin kananan hukumomin jihar Bauchi a ranar Juma'a a shigen jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Osinbajo: Duk Musulmin da ya zabi dan cocin RCCG munafikin Musulunci ne, MURIC

'Karin Bayani: An Gano Ɗan Sheikh Pantami Da Masu Garkuwa Suka Sace.
An Gano Ɗan Pantami Da Masu Garkuwa Suka Sace a Bauchi. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Majiyar ba ta bayyana ko an biya kudin fansa ba.

Al'amin Isa Ali Pantami yana zaune ne tare kakansa

Daily Trust ta tattaro cewa, wanda aka sace din, mai suna Al'amin Isa Ali Pantami, yana zaune ne tare da kakansa.

Da ya ke tabbatar da sako shi, daya daga cikin masu kula da shi ya ce:

"Yanzu muka baro gida; yana gida a yanzu. An gano shi a Dambam, inda wadanda suka sace shi suka ajiye shi. Sun sauke shi a wani shinge daga nan aka kawo shi gida."

Da aka tuntube shi a ranar Juma'a, babban limamin masallacin Isa Ali Pantami, Imam Hussaini, wanda da farko ya ki cewa komai game da lamarin, ya shaida wa Daily Trust cewa "Yaron yana gida."

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya karyata Gwamna Fayemi, ya fadi sirrin da Shugaban kasa ya fada masu

Rundunar yan sandan Jhar Bauchi ta ce ba a kai mata korafi game da sace Al'amin ba

Amma, kakakin yan sandan jihar Bauchi, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ba a kai musu korafi kan lamarin ba.

Wakilin Daily Trust ya nemi ji ta bakinsa game da garkuwar.

"Abin da muke so daga mutane shine su taimaka mana da bayanai masu amfani kan mutanen da ba a yarda da su ba domin mu dauki mataki, kuma idan akwai wata matsala, a kai wa yan sanda rahoto."

Batun garkuwa da mutane ya yi wa al'umma katutu, an sha kira ga gwamnati ta dauki matakan kawo karshen matsalar.

An taba sace dan Ministan Lafiya a 2019

Garkuwa da dan minista mai ci da aka sani ya faru ne a shekarar 2019 a lokacin da aka sace Dayo Adewole, dan ministan lafiya na lokacin, Isaac Adewole.

An sako Adewale bayan awa 24 bayan sace shi a gonarsa da ke Iroko kusa da Fiditi a karamar hukumar Afijio a jihar Oyo.

Kara karanta wannan

'Yan Ta'adda Fiye Da 40,000 Sun Miƙa Wuya Da Sojojin Najeriya, DHQ

A bara, an sace Dapit Karen, yar uwar Ministan Harkokin Mata, Pauline Talen, a Rantiya Lowcosr a karamar hukumar Jos ta Kudu, amma an sako ta bayan awa 48.

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164