Osinbajo: Duk Musulmin da ya zabi dan cocin RCCG munafikin Musulunci ne, MURIC

Osinbajo: Duk Musulmin da ya zabi dan cocin RCCG munafikin Musulunci ne, MURIC

  • MURIC ta yi kira ga al'ummar Musulmin Najeriya kada su bari wani dan cocin RCCG ya dane mulki a Najeriya
  • Wannan ya biyo bayan kafa kwamitin siyasa da cocin ta kafa a rassanta dake fadin tarayya
  • Kungiyar MURIC tace duk Musulmin da ya zabi dan cocin RCCG munafikin addini ne

Bauchi - Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta gargadi jam'iyyun siyasa kada su sake su baiwa wani dan cocin Redeemed Church of Christ Group (RCCG) tikitin takara a zabe.

MURIC ta yi wannan gargadi ne a jawabin da shugabanta na shiyar Bauchi, Safiyanu Gambo, ya saki kuma Legit ta samu.

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, wanda har yanzu bai bayyana niyyar takararsa ba babban Fasto ne a cocin RCCG.

Kara karanta wannan

Mun Bankaɗo Tushen Harin Da Ya Yi Sanadin Kashe Shugaban Miyetti Allah, Rundunar 'Yan Sanda

Ana kyautata zaton cewa nan ba da dadewa ba zai ayyana takararsa.

MURIC
Osinbajo: Duk Musulmin da ya zabi dan cocin RCCG munafikin Musulunci ne, MURIC Hoto: iMedia
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar MURIC, Cocin RCCG na son ganin bayan Musulunci a Najeriya kuma duk Musulmin da ya goyi bayansu makiyin addini ne.

Tace:

"Wajibi ne mu hada kai kafin RCCG ta kawar da Musulmai da sauran darikokin Kirista."
"Abinda yan uwa Musulumai ke fuskanta a kasar Yarbawa inda ake mayar da su saniyar ware duk da sune mafi rinjaye ya isa izina garemu mu san cewa idan yan cocin RCCG suka zama masu mulkin kasar nan."
"Mu a Arewa muna lura da wannan abu. Ba zamu taba yarda dan cocin yaci zabe ba."

Kada ka yaudari Tinubu, idan ba haka ba karshenka ba zatayi kyau ba: Fasto ga Osinbajo

A wani labarin kuwa, fasto Isaac Moses na cocin Amazing Revelation Divine Ministry, Suleja, jihar Niger, ya gargadi mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, kada ya yaudari Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Peter Obi: Ya Zama Dole a Bar Kudu Maso Gabas Ta Mulki Najeriya a 2023

Faston ya bayyana cewa idan Osinbajo ya yaudari Tinubu, hakan na iya zama karshen siyasarsa.

Ya shawarci Osinbajo cewa yaudara zunubi ne kuma a matsayinsa na Fasto ya san da haka, rahoton DailyPost.

Yana koro aya daga littafin Bible, ya gargadi Osinbajo cewa kada "ka yaudari wani."

Asali: Legit.ng

Online view pixel