Karshen Mako: Yadda yan bindiga suka ɓarnata rayuka 62, sace wasu 62, suka kona gida 70 a Kaduna da Zamfara

Karshen Mako: Yadda yan bindiga suka ɓarnata rayuka 62, sace wasu 62, suka kona gida 70 a Kaduna da Zamfara

  • A karshen makon nan da ya gabata, yan ta'adda sun zafafa kai hare-hare kan mutane a jihohin Zamfara da Kaduna
  • Alkaluma sun nuna cewa akalla mutum 62 ne suka mutu, aka sace wasu 62, kuma gidaje sama da 70 suka kone
  • Gwamnatin Kaduna ta saka dokar kulle a kananan hukumomi 2, Zamfara kuma ta bada umarnin tallafawa mutane

Matsalar tsaron da ta addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya ta laƙume rayukan mutane sama da 60 a baya-bayan nan a jihohin Kaduna da Zamfara.

Punch ta rahoto cewa akalla mutum 25 ciki har da sojoji biyu, ɗan sanda da ake zargin ya harbi mai wucewa, akalla gidaje 70 suka kone biyo bayan harin yan ta'adda, ranar Lahadi a Kaduna.

Yan ta'addan sun aikata wannan mummunar ta'asa ne a ƙauyen Agban Kagoro dake ƙaramar hukumar Kaura a kudancin jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamna El-Rufai ya sanya dokar hana fita a Jema'a da Kaura a jiharsa

A jihar Zamfara kuwa, yan bindiga sun halaka 37 kuma suka sace wasu 62 a ƙauyukan Juyi da Doruwa dake karamar hukumar Bungudu.

Haka nan kuma wasu mutum 20 sun rasa rayukan su a ƙauyen Ganar-Kiyawa dake ƙaramar hukumar Bukkuyum duk a Zamfara.

Kaduna da Zamfara
Yadda yan bindiga suka aikata mummunar ɓarna a Zamfara da Kaduna, suka kashe mutum 62, suka sace 62 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ko ya al'umma suka ji da hare-haren?

Kashe-kashen Kaduna ya haddasa wata zanga-zanga ranar Litinin, matasan ƙabilar irate daga yankunan da lamarin ya shafa suka toshe hanya kuma suka farmaki matafiya.

Rahoto ya nuna cewa sun cinnawa wata motar haya Bus wuta lokacin zanga -zanga, wani ɗan sanda da ya musu tirjiya ya saki harbi cikin matasan, ya samu ɗayansu.

Hakan ya tilasta wa gwamnatin Kaduna ƙaƙaba dokar kulle ta tsawon awanni 24 a kananan hukumomin Jema'a da kuma Kaura.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, shi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar jiya Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari Zamfara, sun sheke dagacin kauye da wasu mutum 19

Yace wannan matakin zai ba jami'an tsaro damar yin aikin su na ceton rayuka da dukiyoyin al'umma, kuma su dawo da doka da oda.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamna Malam El-Rufai ya yi Allah wadai da rikicin, wanda ya lakume rayukan mutane, kuma ya salwantar da dukiyoyi.

Sanarwan ta ce:

"Bayan shawari daga hukumomin tsaro, Gwamnatin Kaduna (KDSG) ta saka dokar kulle na awanni 24 a Jema'a da Kaura kuma zata fara aiki nan take. Mun yi haka ne don ceton rayuka da dukiyoyi, da dawo da doka da oda."
"Gwamnatin na kira da mazauna yankunan su bai wa jami'an tsaro haɗin kai a kokarin da ake na dawo da zaman lafiya da bin doka da oda. Gwamnati ta yi Allah wadai da abun da ya auku a wannan yankuna."

Sarakuna ma ba su tsira ba

Basaraken Kukum, a yankin masarautar Kagoro, Jashua Kagoya, wanda ya sha da kyar, ya ce yan bindigan sun shigo a motar Sojoji ɗauke da muggan makamai.

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ya lakaɗa wa Matarsa dukan kawo wuka har Lahira kan karamin abu

A cewarsa, mutane sun dawo gida bayan ayyukan su na yau da kullum da karfe 8:00 na dare, suka fara jin ƙarar harbe-harbe, bisa dole suka tsere.

Kagoya ya ce:

"Kamar yadda kuke gani, sun kona mun gida na ƙurmus, amma duk da haka na gode Allah tun da iyalaina da ni kaina mun tsira daga harin. Ba mu ji daɗi ba, muna kira ga gwamnati ta tashi tsaye wajen kare mutane."

Basaraken ya ce yanzu haka sun gano gawarwakin mutum 23, kuma ana cigaba da binciken sauran mutane.

Wani mazaunin yankin, Derek Christopher, ya ce maharan sun zo da yawa kuma cikin motar Sojoji, Motocin Bas da kuma Babura.

Ya ƙara da cewa:

"Maharan sun kashe sojoji biyu, tun kafin yanzun mafi yawan mutane ba su iya zuwa gonakinsu sbaoda tsoro. Muna kiran gwamnati ta ƙara jibge mana jami'an tsaro domin tabbatar da kare rayuwar mutane."

Yadda Mutanen Zamfara suka ji da harin

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari Kaduna, sun tattara maza da mata 47

Wani ɗan asalin garin Bungudu a Zamfara, Sani Ibrahim, ya ce yan ta'addan a kan Mashina sun farmaki kauyukan Juyi da Dorawa da karfe 2:00 na dare, suka kashe 17, suka sace wasu 62.

Ibrahim ya ce yan ta'addan ɗauke da muggan makamai, sun buɗe wuta kan duk mutumin da suka ci karo da shi lokacin da suka shiga ƙauyukan.

Ya bayyana cewa:

"Sun zo kauyen mu da karfe 2:00 na daren ranar Asabar, suka buɗe wuta nan take kan duk wanda suka gani. Na samu sa'ar guduwa ƙauyen Bingi saboda ba su ganni ba na ɓuya a bayan Bishiya, sun kashe ɗana."

Ya ƙara da cewa baki ɗaya ƙauyukan sun tashi, domin mutanen ciki sun bar gidajen su. Ban da 62 da suka sace, a baya akwai mutum 50 dake hannun su.

Wani mazaunin Bukkuyum, Muhammed Isa, ya ce yan ta'adda sun kashe mutum 20 a ƙauyen Ganar-Kiyawa.

A cewar Isa, maharan sun mamaye ƙauyen da karfe 9::00 na safe, suka kashe mutum 20, suka jikkata wasu da yawa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun mamayi Jami'an gidan Yari, sun halaka fiye da ɗaya

Wane matakin gwamnatin Zamfara ta ɗauka?

A wata sanarwa, kakakin gwamnan Zamfara, Zailani Bappa, yace gwamna Bello Matawalle ya yi matuƙar bakin ciki da sabbin hare-haren yan bindiga.

A sanarwan, an jiyo Matawalle na cewa lamarin abun takaici ne kuma ya zo dai-dai lokacin da zaman lafiya ke dawowa a faɗin jihar. Ya ƙara da cewa ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da tsaro a Zamfara.

Da yake jajantawa iyalan waɗanda suka rasu, gwamnan ya umarci ma'aikatar jin ƙai da walwala ta gaggauta kai wa mutane ɗauki domin su rage raɗaɗi.

A wani labarin kuma Yadda wani ɗan kasuwa ya halaka yan bindigan da suka yi garkuwa da shi, ya dawo gida lafiya

Wani ɗan kasuwa a Ondo ya yi jarumta a sansanin yan bindiga ya kashe mutum biyu yayin da bacci ya ɗauke su.

Bayanai sun nuna cewa mutumin ya yi kamar yana bacci mai nauyi, suma suka kwanta sai ya tashi ya ɗauki makamansu.

Kara karanta wannan

Mafarauci ya bindige tsohon shugaban APC har Lahira, ya ce ya ɗauka wata dabba ce

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262