Wata kungiya a Kaduna ta koka yayin da yan bindiga suka kashe mutum 5 da sace wasu 16
- An rahoto cewa yan bindiga sukn kashe mutane biyar sannan suka yi garkuwa da wasu da dama
- Shugaban wata kungiya ta kula da harkokin tsaro da shugabanci na gari, Ibrahim Abubakar Nagwari, ne ya tabbatar da hakan
- Ya ce lamarin ya afku ne a lokaci daban-daban a tsakanin ranar14 da 19 ga watan Maris
Kaduna - Yan bindiga sun kashe mutane biyar ciki harda wani malamin makaranta a hanyar Layin Lasan Tabanni da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
An tattaro cewa yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutane 16 a kauyukan Dogon Dawa, Layin Mahuta, da Tabanni da ke yankin gabashin karamar hukumar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar kula da harkokin tsaro da shugabanci na gari, Ibrahim Abubakar Nagwari.
Kungiyar ta ce lamarin ya afku ne a lokuta mabanbanta tsakanin 14 da 19 ga watan Maris, Daily Trust ta rahoto.
Kungiyar ta bayyana cewa a ranar 14 ga watan Maris, yan bindiga sun kashe wani Haruna Tanko Dogon Dawa da wasu mutane biyu a hanyar Dogon Dawa- Zaria.
Nagwari ya ce:
“An kuma yi garkuwa da wasu mutane takwas a wannan hanyar. A Layin Mahuta (Tabanni), an kashe wani Abdullahi Abubakar wanda yake malamin makaranta ne a hanyar Layin Lasan Tabanni a ranar 16 ga watan Maris.
“A ranar 17 ga watan Maris, an kashe wani tsoho dan shekara 70 sannan aka sace wasu mata bakwai a Layin Mahuta Tabanni. An kuma yi garkuwa da wasu biyu a tsohon Tabanni.”
Shugaban kungiyar ya kara da cewar a yankin Randagi, yan bindiga sun saki mutane 32 daga cikin 46 da suka sace a makonni uku da suka gabata a Unguwar Bula da Ijinga bayan an biya kudin fansa naira miliyan 16.
Ya bukaci jami’an tsaro da su dunga amsa kiran gaggawa a kewayen gudunmar Dogon Dawa, Kuyello, Tabanni, Kutemashi da Birnin Gwari, rahoton The Nation.
Sai dai kuma, shugabar karamar hukumar, Hajiya Ummah K. Ahmed, wacce ta tabbatar da kisan malamin da raunata wani, ta ce bata san da labarin sauran hare-haren da sace-sacen mutane da kungiyar ta ambata ba.
Yan sanda sun kashe yan bindiga 4, sun gano bama-bamai 5 da ba a tayar ba
A wani labari na daban, rundunar yan sandan jihar Imo ta kashe yan bindiga biyar da ake zaton yan kungiyar awaren IPOB ne a wani musayar wuta da suka yi a safiyar Lahadi, 20 ga watan Maris.
Lamarin ya faru ne lokacin da yan bindigar suka je kai farmaki ofishin yan sanda da ke karamar hukumar Oru East a jihar Imo.
Kakakin yan sandan jihar, Micheal Abattam, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Owerri, babbar birnin jihar, jaridar Vanguard ta rahoto.
Asali: Legit.ng