Maza 115 da mata 19 na shafa wa kanjamau, kuma ban gama ba, Kyakyawar budurwa

Maza 115 da mata 19 na shafa wa kanjamau, kuma ban gama ba, Kyakyawar budurwa

  • Wata budurwa 'yar Najeriya ta bayyana yadda ta shafa wa maza 115 da mata 19 cutar kanjamau bayan kamuwarta
  • Budurwar ta sanar da hakan ne yayin da take martani ga wata wallafar budurwar da tace ta kwashe shekaru hudu tana fama da cutar
  • Budurwar ta sanar da cewa babban abokin yayanta ne ya fara saninta mace kuma shi ne ya shafa mata muguwar cutar, inda za ta cigaba da saka wa wasu

Wata budurwa 'yar Najeriya ta bayyana yawan mutanen da ta shafa wa cutar kanjamau bayan ta gano tana da cuta mai karya garkuwar jiki a shekarar 2016.

Ta yi wannan bayanin ne a Twitter bayan wata ma'abociyar amfani da Twitter ta sanar da yadda take rayuwa da cutar tsawon shekaru uku bayan ta same ta.

Maza 115 da mata 19 na shafa wa kanjamau, kuma ban gama ba, Kyakyawar budurwa
Maza 115 da mata 19 na shafa wa kanjamau, kuma ban gama ba, Kyakyawar budurwa. Hoto daga Avert.org
Asali: UGC

@NellyNesh19 ta bayyana cewa ta samu cuta mai karya garkuwar jikin yayin da take da shekaru 21 a duniya kuma yanzu shekarunta 24.

Kara karanta wannan

Bidiyon jaruma Umma Shehu tare da diyarta yayin da suke girgijewa ya haifar da cece-kuce

Ta rubuta: "Na samu cutar kanjamau inda da shekaru 21 kuma yanzu shekaru na 24 sannan ina rayuwata lafiya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin martani kan wallafar, wata budurwa 'yar Najeriya mai amfani da suna @the_afropolite ta ayyana cewa ta samu cutar ne ta wurin abokin yayanta a 2016 lokacin da take da shekaru 18 a duniya.

Ta kara da cewa a shekarar 2017 ta gane tana da cutar kuma ta sha alwashin gogawa wasu abinda aka bata ba tare da kwaroron roba ba.

Budurwar ta kara da ikirarin cewa ta gogawa maza 115 cutar tare da mata 19 a halin yanzu kuma ba ta gama ba.

Ta rubuta:

"Na samu cutar ta wurin babban abokin yayana a 2016 lokacin da nake da shekaru 18 kacal. Shi ne namiji na farko da na fara sani har zuwa lokacin da na cika shekaru ashirin a duniya. A watan Disamban 2017 na gane ina dauke da cutar. Daga nan na sha alwashin rabawa mutane. A yanzu na sanya wa maza 115 da mata 19 kuma ban gama ba.

Kara karanta wannan

Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana

"Kafin nan, ban damu ba idan na mutu a yau. Rayuwata bata da amfani duk da na kammala karatu amma na kasa samun aiki. Me ye amfanin rayuwar idan zan dogara da maza kan kowanne kudi da nake bukata. Rayuwa babu amfani idan kullum sai na sha kwayoyin ARV.
"Kuna tunanin kuna da karfin halin kirana muguwa? Idan da kun san Ifeanyi, mugun abokin yayana, da ba ku kira ni da muguwa ba. Tunda babu wani bankin Najeriya da ke son bani aiki a matsayina na kwararriyar ma'aikaciyar banki. Don haka dole in yada cutar.
"Idan namiji, yarinya ko 'yar madigo da ta kasa rike bukatar ta, ban damu ba idan zan basu sau dari. Kudi gare ni, nishadi kuma in raba musu cuta."

Asali: Legit.ng

Online view pixel