Duk da Buhari Landan yake zuwa jinya, ya saki N10bn don gina sabon asibiti a Aso Rock

Duk da Buhari Landan yake zuwa jinya, ya saki N10bn don gina sabon asibiti a Aso Rock

  • Yan majalisar dokokin tarayya sun ziyarci ginin sabon asibitin shugaban kasa da ake yi a Aso Rock
  • Kawo yanzu, Shugaba Buhari ya saki Naira bilyan goma don fara ginin asibitin wanda manya zasuyi amfani da shi
  • Wanda aka baiwa kwangilan ginin Oliver Berger, ya bada tabbacin cewa za'a kammala ginin akan lokaci

Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta bayyana cewa ta saki N10.06 billion kawo yanzu cikin kudin gina sabon sashen manyan mutane a asibitin fadar shugaban kasa, Aso Rock Abuja.

Kamfanin dake ginin asibiti shina Julius Berger Plc.

Sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar, ya bada tabbacin cewa za'a kammala ginin kawo ranar 31 ga Disamba, 2022, rahoton Vanguard.

Aso Rock
Duk da Buhari Landan yake zuwa jinya, ya saki N10bn don gina sabon asibiti a Aso Rock Hoto: Presidency
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Makusantan Kwankwaso sun lallaba sun gana da Shekarau, suna kokarin sake jawo shi PDP

Ya bayyana hakan ne ga kwamitin majalisar dattawa suka kai ziyarar ganin ido asibitin.

Tijjani Umar ya bayyana cewa tun 2021 da aka fara ginin, an baiwa dan kwangila N10.06 billion.

Yace da farko an biya N416.6 million, N1.06 billion a 2021, kuma cikin N20.8bn da aka tanadi kashewa a 2022, an biya N8.5bn.

Mambobin majalisar dattawan da suka tafi ziyarar sun hada da Istifanus Gyang (PDP- Plateau North) , Mpigi Barinada (PDP-Rivers South-East), Tofowomo Nicholas (PDP-Ondo South), Nmachi Ama (PDP-Ebonyi South), Gershon Bassey (PDP-Cross River South), Bulus Amos (APC-Gombe South), Dimka Ayuba (APC-Plateau Central), Frank Ibezim (APC-Imo North APC) da Halliru Jika (APC-Bauchi Central).

Manajan Julius Berger da yayi yawo da yan majalisan, Oliver Berger, ya basu tabbacin cewa za'a kammala ginin akan lokaci.

An yi bikin fara ginin Asibitin Alfarma na kudi N21.9bn mai gado 14 a Aso Rock

Zaku tuna lokacin da muka kawo muku labarin cewa Shugaban ma'aikatan fadar Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba, 2021 ya jagoranci bikin kaddamar da ginin asibitin alfarma mai gao 14 kacal a fadar Aso Villa.

Kara karanta wannan

APC ta gamu da gagarumin cikas a wata jihar kudu yayin da kansiloli 5 suka fice, sun koma PDP

Wannan asibiti da za'a gina zai ci akalla bilyan 21.

A jawabin da ya gabatar a bikin fara ginin, Gambari ya bayyana cewa idan aka kammala ginin wasu zababbun mutane zasu amfana da katafaren asibitin, rahoton Thisday.

A cewarsa, Shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa da iyalansu da kuma wasu jami'an gwamnati zasu yi amfani da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel