Shehu Sani: Duk mai sha'awar shiga yakin Ukraine kuma bai da $1k na biza, ya zo Arewa ya nuna kwarewarsa

Shehu Sani: Duk mai sha'awar shiga yakin Ukraine kuma bai da $1k na biza, ya zo Arewa ya nuna kwarewarsa

  • Sanata Shehu Sani ya ce yan Najeriya da ke son zuwa Ukraine domin yakar dakarun rasha amma basu da dala 1000 na kudin biza suna iya komawa arewa
  • Tsohon sanatan na Kaduna ya ce su zo yankin domin nuna kwarewarsu a yaki da Boko Haram da yan fashin daji
  • Ya ce anan kwarewar tasu za ta yi amfani sosai kuma ba sa bukatar biyan ko sisin kwabo a nan

Tsohon dan majalisa da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya, Sanata Shehu Sani ya shawarci yan Najeriya da ke da sha’awar shiga yakin Ukraine da Rasha amma kuma basu da kudin biza.

Sanata Sani ya bukace su da su koma yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabashin Najeriya domin nuna kwarewarsu.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Ba za mu bari 'yan Najeriya su tafi Ukraine yaki ba, gwamnatin Buhari

Shehu Sani: Duk mai sha'awar shiga yakin Ukraine kuma bai da $1k na biza, ya zo Arewa ya nuna kwarewarsa
Shehu Sani: Duk mai sha'awar shiga yakin Ukraine kuma bai da $1k na biza, ya zo Arewa ya nuna kwarewarsa
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa wannan bajinta nasu zai yi matukar amfani wajen yaki da Boko Haram da yan fashin daji sannan kuma cewa basa bukatar biyan kudi a nan.

Mai aniyar takarar gwamnan jihar Kaduna a zaben 2023, ya bayar da wannan shawara ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, a ranar Litinin, 7 ga watan Maris.

Tun farko dai kimanin matasa 115 ‘yan Najeriya, a ranar Talata, 1 ga watan Maris, sun nuna sha'awar shiga yakin kasar Ukraine da Rasha.

Sai dai kuma ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya ya ce 'yan Najeriya da ke son zuwa Ukraine don yakar sojojin Rasha dole ne su amince da biyan dala 1,000 (kwatankwacin N560,000) kowannen saboda a samar musu da tikiti da biza.

Kara karanta wannan

A tura su Borno: Jami'in tsaro ya nemi a tura matasan da ke son zuwa Ukraine yaki su yaki Boko Haram

Sani ya rubuta:

“Wadanda ke sha’awar zuwa Ukraine da yakar yan Rasha kuma basu samu zuwa ba saboda dala 1000 na kudin biza, suna iya komawa yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabashin Najeriya da zama inda kwarewarsu za ta yi amfani a yaki da Boko Haram da yan fashin daji; ba a bukatar wani kudi a nan.”

Ku fara da Boko Haram, tsohon shugaban yan sanda ga yan Najeriya da ke son tunkarar sojojin Rasha

A wani labari makamancin haka, mataimakin sufeto janar na yan sanda mai ritaya, Adedayo Adeoye, ya bayyana cewa ya kamata a tura sojojin da aka kora wadanda suka nuna shirinsu na yakar sojojin Rasha da suka kai mamaya Ukraine zuwa Borno, Yobe da sauran jihohin arewa maso yamma domin yakar yan ta’adda.

Adeoye ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar The Punch a ranar Juma’a, 4 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Ku fara da Boko Haram, tsohon shugaban yan sanda ga yan Najeriya da ke son tunkarar sojojin Rasha

A cewarsa, ya kamata gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye wajen zaburarwa da dawo da sojojin da aka kora domin karfafa yakin da ake yi da Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng