Gwanda in zama dan gudun Hijra da in dawo Najeriya, Dan Najeriya dake Ukraine

Gwanda in zama dan gudun Hijra da in dawo Najeriya, Dan Najeriya dake Ukraine

  • Gwamnatin tarayya na cigaba da jigilar yan Najeriya mazauna kasar Ukraine da yaki ya rutsa da su
  • Duk da haka, wasu yan Najeriya sun bayyana cewa gwanda yaki ya cisu da su dawo gida Najeriya
  • Gwamnati ta ce duk wadanda suka ki hawa jirgin dawo da su babu abinda gwamnati zata iya musu kuma

Wani dan Najeriya mazaunin Ukraine, Nnamdi Okafor, ya bayyana cewa ya gwammace ya zama dan gudun Hijra a wata kasa da yawo gida Najeriya.

Okafor ya bayyana hakan a hirarsa da jaridar TheNiche ranar Juma'a.

Okafor, dan asalin jihar Anambra ne yana zama birnin kasar Ukraine, Kiev.

Ukraine
Gwanda in zama dan gudun Hijra da in dawo Najeriya, Dan Najeriya dake Ukraine
Asali: Twitter

Yayinda aka tambayesa shin meyasa bai biyo jiragen kawo yan Najeriya gida da gwamnatin tarayya ta dau nauyi ba, yace:

"Me zan koma yi Najeriya? Shin akwai abinda ya canza ne?"
"Yanzu ina nan daram dam a Ukraine. A birnin kasar nike zama, Kyiv, amma na koma wani garin dake bakin boda wanda a'a fara kai hari ba."
"Amma idan yaki ya iso nan, zan koma wata kasa da yardan Allah. Amma idan wannan ce ajali ne, na yarda. Gwanda in zauna matsayin dan gudun Hijra da in koma Najeriya."

Na Gwammace In Biya N415,000 in Tafi Ukraine In Zama Bawa, Ɗan Najeriya Ya Yi Ɓaɓatu A Bidiyo

Wani mazaunin garin Abuja ya koka akan mawuyacin halin da Najeriya take ciki inda yace ya gwammaci ya biya $1,000 wato N415,000 a matsayin kudin jirgi don ya shiga cikin sojojin Ukraine maimakon ya tsaya a Najeriya.

Ofishin jakadancin Ukraine ta sakataren su na biyu, Bohdan Solty a ranar Alhamis, 3 ga watan Maris ta bayyana yadda suka shirya tsaf wurin kwashe duk wasu ‘yan Najeriya da ke shirin tafiya kasar amma da sharadin kawo $1,000 don kudin jirgi.

Yayin tattaunawa da Legit TV inda aka yi masa tambayoyi, mutumin ya caccaki Buhari akan ba kasar Afghanistan $1m yayin da kungiyar malaman jami’a, ASUU take tsaka da yajin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel