Labari mai dadi: 'Yan Najeriya sun samu mafaka a kasashe biyu da ke makwabtaka da Ukraine

Labari mai dadi: 'Yan Najeriya sun samu mafaka a kasashe biyu da ke makwabtaka da Ukraine

  • ‘Yan Najeriya da ke makale a kasar Ukraine tun bayan barkewar yaki, an ce su nemi mafaka tare da bin hanyar da za ta dawo dasu gida Najeriya
  • A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren din-din-din na ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, an ce 'yan kasar su je kan iyakokin kasashen Hungary da Romania.
  • Sanarwar ta biyo bayan wani rahoto ne da aka tabbatar da cewa gwamnatocin kasashen biyu sun bai wa ‘yan Najeriya da ke Ukraine damar shiga kasashensu ba tare da biza ba

FCT, Abuja - Gwamnatocin Romania da Hungary sun amince da shigowar 'yan Najeriya mazauna Ukraine ba tare da biza ba a daidai lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine.

Gwamnatin tarayya ta sanar da wannan labari mai dadi ne ta hannun ma’aikatar harkokin wajen kasar a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Ukraine da Rasha za su yi zaman tattaunawar sulhu, an fadi inda za a gana

Najeriya da Ukraine na magana kan ci dawo da 'yan Najeriya gida
Labari mai dadi: 'Yan Najeriya sun samu mafaka a kasashe biyu da ke makwabtaka da Ukraine | Hoto: Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya
Asali: Facebook

A cikin sanarwar da Ambasada Gabriel Aduda ya sanya wa hannu, an shawarci ‘yan Najeriya mazauna Ukraine da su gudu zuwa iyakar kasar Zahony ta Hungary da kuma iyakokin Suceava, Tulcea, Satu Mare County, da kuma Maramures.

Aduda, wanda shi ne sakataren din-din-din a ma'akatar harkokin wajen Najeriya ya tabbatar wa ‘yan kasar cewa ma’aikatar na daukar isassun matakai domin dakile dimbin kalubalen da suke fuskanta, musamman a kokarin tsallakawarsu zuwa kasar Poland.

Sanarwar da The Cable ta ce ta samu, Legit.ng Hausa kuma ta nakalto ta shaida bayanan Aduda, inda yake 'yan Najeriya za su iya shiga cikin kasashen biyu da aka ambata ba tare da biza ko takardun izinin shiga ba.

Hakazalika, sanarwar ta bayyana irin kokarin ministan harkokin wajen Najeriya ke yi wajen tattaunawa da takwaransa na kasar Ukraine don tabbatar da tsaron 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja

Wani yankin sanarwar ya ce:

“Mai girma Ministan Harkokin Waje ya tattauna da takwaransa, Ministan Harkokin Waje na Ukraine kan wadannan abubuwa marasa dadi kuma dukkansu suna aiki don rage radadin da ‘yan Najeriya ke ciki, ciki har da tura Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) zuwa kan iyaka don tabbatar da samun saukin kubuta ga dukkan ‘yan Najeriya da ‘yan sauran kasashe”.

Aisha Buhari ta mika kokon bara ga Buhari a madadin 'yan Najeriya

A wani labarin, kokarin da jami’an diflomasiyyar Najeriya ke yi na ganin an kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Ukraine da yaki ya dumfara ya sha yabo daga Aisha Buhari.

Sai dai, a cikin wani sakon da ta wallafa a Facebook a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, uwargidan ta shugaban Najeriya ta yi kira ga kwamitin shugaban kasa kan yaki da Korona da ta yafe kudin gwajin Korona ga 'yan Najeriyan da suke dawowa daga kasashen Turai.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya gana da daliban jihar Sokoto da ke Ukraine, ya bukaci iyaye da su kwantar da hankalinsu

Ta kuma roki a soke karbar irin wadannan kudade ga duk yaran Najeriya da ke dawowa gida nan ba da dadewa ba, tare da rage kudin gwajin ga dukkan ‘yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.