An yi kus-kus tsakanin Sarkin Kano da takwaransa na Katsina

An yi kus-kus tsakanin Sarkin Kano da takwaransa na Katsina

  • Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, da na Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, sun yi wata tattaunawar sirri
  • Sun saka labulen ne a fadar sarkin Katsina a ranar Lahadi, inda suka shafe kimanin awa daya da rabi suna zantawa
  • Ana ganin ganawar tasu ba za ta rasa nasaba da murabus din Wazirin Katsina, Farfesa Lugga ba

Katsina - Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi wata ganawar sirri tare da takwaransa na Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu.

Ganawar wacce ta shafe fiye da awa daya da rabi, daga 12.30 zuwa 2:05 na rana ya gudana ne a fadar sarkin Katsina, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wazirin Katsina ya yi murabus daga kan kujerarsa bayan wata takaddama da ta biyo jawabinsa a Ilorin

An yi kus-kus tsakanin Sarkin Kano da takwaransa na Katsina
An yi kus-kus tsakanin Sarkin Kano da takwaransa na Katsina Hoto: Dailypost
Asali: UGC

Babu cikakken bayani kan ganawar tasu a daidai lokacin kawo wannan rahoton, amma akwai hasashen cewa ba zai rasa nasaba da shigowar majalisar kolin Musulunci cikin batun murabus din Wazirin Katsina, Farfesa Sani Abubakar Lugga ba.

Lugga dai ya yi murabus bayan tuhumar da majalisar ta yi masa kan cewa ya tattauna batutuwan rashin tsaro a Ilorin, jihar Kwara, ba tare da yardar masarautar ba.

A ranar 14 ga watan Fabrairu ne Farfesa Lugga ya halarci wani taro a Ilorin inda ya bayyana cewa yawan hare-haren yan bindiga ya yi sanadiyar rufe makarantu a kananan hukumomi takwas na jihar Katsina.

Sai dai, hakan bai yiwa majalisar masarautar Katsina dadi ba, inda ta aike masa da tuhuma.

A takardar da yake martani ga tuhumar da aka masa, Farfesan ya amsa lamura uku da majalisar ke tuhumarsa a kai sannan daga bisani ya gabatarwa Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman takardarsa ta ajiye sarautarsa.

Kara karanta wannan

Ayiriri: Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya za ta shiga daga ciki a ranar Juma'a mai zuwa

Daily Trust ta kuma rahoto cewa wata majiya da ta yi magana kan ziyarar na sarkin Kano, ta ce wasu manyan arewa da ke rike da sarauta ne suka wakita basaraken domin ya shiga tsakani kan batun murabus din.

Ba a sani ba ko an cimma matsaya tsakanin sarakunan biyu a yayin tattaunawar, amma wata majiya ta ce zuwan sarkin Kano jihar babban dalili ne na cimma matsaya mai kyau.

Jim kadan bayan taron, sarkin Kanon ya daga zuwa jaharsa da misalin karfe 3:00 na rana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel