An damke wani mataimakin Sufritandan yan sanda ASP na bogi

An damke wani mataimakin Sufritandan yan sanda ASP na bogi

  • Yan sanda sun yi arangama da wani jami'in ASP amma na bogi yana raka motar magunguna
  • Kaakin hukumar yan sanda ta bayyana cewa daga yanayin sanya kayansa ka san akwai abin zargi
  • Kaakin hukumar yan sandan jihar ta ce za'a gurfanar da shi a kotu idan aka kammala bincike

Ondo - Jami'an hukumar yan sandan jihar Ondo sun damke wani mutumi mai suna Nkanu Patrick wanda ke ikirarin shi mataimakin Sufritanda ASP ne.

TVCNews ta ruwaito cewa jami'an yan sandan yankin Ore dake yawon sintiri suka damke mutumin a babban Benin/Ore Expressway.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, ta ce an damkeshi ne yana raka wata mota kirar Volkswagen dauke da magunguna inda suka nufi birnin Benin.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan Sanda Sun Kama Wata Hajiya Fatima Da Ke Yi Wa 'Yan Ta'adda Safarar Layyu Da Leƙen Asiri

An damke mataimakin Sufritandan na yan sanda ASP na bogi
An damke mataimakin Sufritandan na yan sanda ASP na bogi Hoto: TVC Newsng
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tace yana sanye da kayan sarki don basaja amma kayan Sarkin suka janyo hankalin yan sanda suka tsayar da shi don bincikensa.

A cewarta, ya kasa bayar da gamsasshen bayani kan kasancewarsa dan sanda.

Ta ce za'a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike.

An damke wani jami'in dan sandan bogi mai amfani da kayan sarki yana damfarar mutane

Haka a jihar Ogun makon da ya gabata yan sandan jihar Ogun suka damke wani mutumin dan shekara 38, mai suna, Akinyemi Thomas, kan laifin ikirarin zama dan sanda.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ta bayyana hakan a jawabin ta saki a Abeokuta, birnin jihar.

A cewarta:

"An damke mutumin ne lokacin da yan sandan yankin Shagamu suke gudanar da sinitiri tare da DPO CSP Godwin Idehai."

Kara karanta wannan

An damke wani jami'in dan sandan bogi mai amfani da kayan sarki yana damfarar mutane

"Sun hango mutumin sanye da kayan sarki karkashin gadar titin Legas-Ibadan."

Asali: Legit.ng

Online view pixel