Fashin bankin Edo: Bidiyon yan bindiga yayin da suke fita da buhu-buhu na kudi
- Wani bidiyo ya bayyana kan fashin da yan bindiga suka yi a wasu bankuna a jihar Edo
- A cikin bidiyon wanda ke yawo a shafukan soshiyal midiya, an gano yan fashin dauke da buhuhunan kudi yayin da suke fita da su daga bankin zuwa motocinsu
- A ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu, ne maharan suka farmaki wasu bankuna hudu a jihar, inda suka kashe akalla mutane bakwai
Edo - An gano yan bindigar da suka farmaki bankuna a Uromi, hedkwatar karamar hukumar Esan North-East da ke jihar Edo, a ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu, suna fita da kudade a buhu-buhu.
Akalla mutane bakwai ciki harda jami’an yan sanda biyu aka kashe a farmakin.
Yan bindigar dai sun kai farmakin nasu ne a wasu bankunan zamani guda hudu.
A wani bidiyo na lamarin wanda ke yawo yanzu haka a soshiyal midiya, an gano yan fashin suna loda buhuhunan kudaden da suka sato daga bankunan a bayan motocinsu, Daily Trust ta rahoto.
Yan fashin sun yi tuki dukka bangarori biyu na titin yayin da suke zuba kudaden da suka sata a cikin motocinsu, ciki harda wata motar Toyota Corolla ja, rahoton Premium Times.
An gano daya daga cikinsu yana harbi a iska yayin da sauran suka fitar da buhuhunan daga wani banki.
An rahoto cewa sun shafe fiye da awa biyu suna fashin. Wata majiya ta ce yanfashin sun kai farmakin da misalin 3:30 na rana sannan suka tafi da misalin 6:00 na yamma.
Kalli bidiyon a kasa:
Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki tawagar kwamishina, ya sha sudin goshi
A wani labari na daban, a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu, an shiga tashin hankali a Enugu bayan da aka samu labarin cewa, kwamishinan filaye na jihar, Mista Chidi Aroh, ya tsallake rijiya da baya bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai masa hari.
Biyu daga cikin jami’an tsaronsa, wadanda suka yi artabu da ‘yan bindigar, ana fargabar sun mutu, saboda har yanzu ba a gano gawarwakinsu ba.
Jaridar Punch ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Fabrairu, yayin da Aroh ke dawowa daga Anambra, inda ya halarci wani taro.
Asali: Legit.ng