Rana ba ta karya: An sa sabon ranar shari’a da ‘Dan Majalisar da ake zargi da takardun ‘bogi’

Rana ba ta karya: An sa sabon ranar shari’a da ‘Dan Majalisar da ake zargi da takardun ‘bogi’

  • ICPC za ta fara shari’a da Mohammed Garba Gololo a babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja
  • Hukumar ta na tuhumar Hon. Mohammed Garba Gololo da laifin yin karya a game da satifiket dinsa
  • Gololo ya fadawa INEC cewa ya samu shaidar BSc da MBA daga Jami’ar LASU, ICPC ta ce karya ne

Abuja - Hukumar ICPC mai binciken masu laifuffuka a Najeriya ta na tuhumar Mohammed Garba Gololo da laifin amfani da takardun digiri na bogi.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 21 ga watan Fubrairu 2022 cewa an shigar da karar Honarabul Mohammed Garba Gololo a kotu.

An maka Mohammed Gololo mai wakiltar mazabar Gamawa a jihar Bauchi a majalisar wakilai ne a babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta amincewa NDLEA ta ci gaba da tsare Abba Kyari da abokan harkallarsa 6

Hukumar ICPC ta fadawa kotun tarayyar cewa takardun shaidar digirin farko da na biyu da Mohammed Gololo yake amfani da su duk na bogi ne.

Bai je LASU ba - ICPC

A takardar karar da ICPC ta shigar a kotun mai zama a babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana cewa Garba-Gololo yana ikirarin ya yi karatu a LASU.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Satifiket din da Mohammed Garba Gololo ya ke amfani da su, sun nuna ya samu digirin B. Sc da kuma digirgir na MBA duk daga jami’ar ta jihar Legas.

Rana ba ta karya: An sa sabon ranar shari’a da ‘Dan Majalisar da ake zargi da takardun ‘bogi’
‘Dan Majalisar Bauchi Hoto: @INECNigeria
Asali: Twitter

Amma ICPC ta ce wadannan satifiket da Honarabul Gololo ya gabatarwa hukumar INEC kafin ya shiga zabe na bogi ne, ba daga jami’ar LASU suka fito ba.

Sahara Reporters ta ce an tsaida 11 ga watan Afrilun 2022 a matsayin ranar da za a fara sauraron karar. Nan da kusan makonni bakwai za a fara shari'a.

Kara karanta wannan

Rikicin fili: ABU Zaria na barazanar kai Gwamna gaban Alkali a dalilin saba umarnin kotu

Hon. Gololo ya ki zuwa kotu

Hakan ya zo ne bayan an gaza gurfanar da ‘dan siyasar a gaban Alkali mai shari’a, K. N. Ogbonnaya na babban kotun tarayyar a unguwar Kubwa.

Gololo ya ki bayyana a gaban kotu, don haka dole Alkali K. N. Ogbonnaya ya dage zaman da ya kamata ayi zuwa ranar 11 ga watan Afrilu domin ya hallara.

Ba yau aka fara maganar ba

Tun ba yau ba aka ji wata kungiya mai suna SIVWOC ta na zargin wasu daga cikin ‘yan siyasan jihar Bauchi da amfani ne da takardun kara tuna bogi.

Daga cikin wadanda ake tuhuma da wannan laifi har da Hon. Garba Gololo. Kungiyar tace bincikenta ya nuna mata Gololo bai yi karatu a LASU ba.

SIVWOC tace ta aikawa jami’ar Legas takarda domin jin ko ta san wani Garba Gololo a matsayin tsohon Dalibin ta, jami’ar tace ba ta san da zaman shi ba.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An yi cacar baki tsakanin mai Shari'a da Nnamdi Kanu kan tufafinsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel