Kungiyar SIVWOC ta kai karar ‘Yan takarar Bauchi gaban Shugaban kasa Buhari

Kungiyar SIVWOC ta kai karar ‘Yan takarar Bauchi gaban Shugaban kasa Buhari

Wata kungiya mai suna SIVWOC da ke kokarin taimakawa rayuwar Mata da kananan yara matasa galihu a Najeriya tana zargin wasu daga cikin ‘yan siyasa na jam’iyyar APC mai mulki a jihar Bauchi da cewa su na amfani ne da takardun bogi.

Kungiyar ta aika takarda ta musamman ga shugaba Muhammadu Buhari ta hannun Safiya Abdullahi Bauchi inda ta jawo hankalin shugaban kasar da cewa wasu daga cikin wadanda su kayi takara a APC a zaben bana su na da kashi a jikin su.

Daga cikin wadannan manyan ‘yan siyasa da aka kawo sunayen su akwai:

1. Halliru D. Jika

Honarabul Halliru Jika mai wakiltar Ganjuwa da Darazo yayi karya wajen bada bayani game da Diflomar da yake ikrari yayi a Kaduna. Kungiyar tace akwai kuma alamun tambaya game da jarrabawar WAEC din da Hon. Jika ya rubuta. Bayan haka kuma dai SIVWOC ta tabbatar da cewa ‘dan siyasar ya zabga karya game da asalin ranar haihuwan sa bila-adadin.

KU KARANTA: Jihohi irin su Kebbi sun manta da menene dauke wuta a mulkin Buhari

2. Muhammad Garba Gololo

Kungiyar nan tace binciken da tayi ya nuna mata cewa Honarabul Garba Gololo mai wakiltar yankin Gamawa bai da Digirin da yake ikirarin yayi a Legas. Kungiyar SIVWOC tace ta aikawa jami’ar Legas takarda domin jin ko ta san wani Garba Gololo a matsayin tsohon Dalibin ta, inda jami’ar ta maida martani cewa ba ta taba jin irin wannan suna ba.

3. Abubakar Dalhatu Abdullahi

Wannan kungiya har wa yau tace Honarabul Abubakar Dalhatu Abdullahi wanda ya nemi ya wakilci Mazabar Bogoro da Dass da kuma Tafawa Balewa yayi karya a game da karatun sa na Firamare. Kungiyar tace ‘Dan takaran yace ya gama Firamare a shekarar 1980, amma an gano cewa sai a cikin 1978 aka kafa wannan makaranta da ya kira a Duniya.

4. Ibrahim Mohammed Baba

SIVWOC tace akwai bukatar a sake duba gaskiyar maganar karatun Bokon da ‘Dan majalisar Katagum watau Hon. Ibrahim Baba yayi domin kuwa a wasu wurare takardun sa sun nuna cewa ya kammala Difloma a 2000 inda a wasu wurare kuma aka ce ya gama ne tun 1994. Haka kuma dai akwai alamun tambaya game da Digirin sa na farko da na biyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel