Jakaden kasar Kenya a Najeriya ya yanke jiki ya fadi, ya rasu a Abuja

Jakaden kasar Kenya a Najeriya ya yanke jiki ya fadi, ya rasu a Abuja

  • Jakadan kasar Kenya a Najeriya, Dr Wilfred Machege ya yanke jiki a cikin gidansa kuma ya rasu a take
  • An gano cewa Machege ya kammala cin abincin rana a ranar Asabar kuma ya fadi ne a yayin da matarsa ke tare da shi
  • An hanzarta garzayawa da shi wani asibiti da ke cikin garin Abuja amma aka tabbatar da mutuwarsa

FCT, Abuja - Jakadan kasar Kenya a Najeriya, Wilfred Machage ya riga mu gidan gaskiya.

A wata takarda da ma'aikatar kula da harkokin waje ta fitar, ta tabbatar da yadda ya yanke jiki ya fadi a gidan shi, inda aka sanar da rasuwar shi a ranar Asabar a asibiti cikin garin Abuja.

Jakaden kasar Kenya a Najeriya ya yanke jiki ya fadi, ya rasu a Abuja
Jakaden kasar Kenya a Najeriya ya yanke jiki ya fadi, ya rasu a Abuja. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

Takardar ta ruwaito:

"Ma'aikatar kula da al'amuran waje tana da na sanin sanar da mutuwar farad daya da Hon. Dr Ambassador Wilfred Machage, jakadan kasar Kenya a Najeriya da sauran kashe 12 a tsakiyar da yammacin Afirika wanda ya yi a yau.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ina shirin aurar da 2 daga cikin 'ya'yana mata da aka sace, Basarake

"Ambassador Machage ya yanke jiki ya fadi a gidansa, inda aka sanar da rasuwar sa a asibiti, jim kadan misalin karfe 12:30 na wannan ranar a Abuja, Najeriya.

Matar shi tana tare da shi a lokacin da lamarin mara dadin ya auku, Vanguard ta ruwaito.

Yayin tabbatar da rasuwar Amb. Machage, babban sakataran Ambasadan, Macharia Kamau ya ce ma'aikatar da kasar sun rasa jajirtaccen shugaba.

Haka zalika, abokin tagwaitakar shi, Sospeter Magita, wanda a baya shi ne tsohon jakadan kasar Kenya a Russai, ya bayyana wa manema labarai yadda jakadan ya yanke jiki ya fadi kuma ya mutu a gidan shi bayan ya ci abincin rana.

Magita ya bayyana yadda dan uwan nashi Gisuka ya rayu cikin koshin lafiya.

"Ina mai alhini da takaici a yau na yi rashin babban abokina kuma mai karfafa ni."

Kara karanta wannan

Kano: Ya Jefa Yaro Cikin Rijiya Bayan Yin Rikici Da Mahaifin Yaron, Kotu Ta Ce a Tsare Shi a Gidan Gyaran Hali

Ya kara da bada labarin yadda dan uwan nasa ya rasu lokacin yana tare da matar sa - wacce suke rayuwa tare a Najeriya.

Idan an tuna, tsohon jakadan Sudan a Najeriya, Tagelsir Ali, ya rasu a Abuja a ranar 24 ga watan Oktoba 2014.

Jakadan Najeriya a kasar Jordan ya kwanta dama

A wani labari na daban, Haruna Ungogo, jakadan Najeriya a kasar Jordan, masarautar Hashmite da ke Jordan da Iraq, inda ya rasu yana da shekaru 75 da haihuwa.

Daily Nigerain sun tattaro bayanai a kan mutuwarsa a ranar Lahadi da safe a asibitin Garki da ke Abuja, bayan kwantar da shi da aka yi da kwana biyar. Majiya daga iyalansa ta ce za a yi jana'izarsa a Kano ranar Litinin.

Yayi aiki da gwamnatin Kano a matsayin sakataren gwamnati, daga baya kuma ya zama shugaban Folitakanik da ke jihar Kano. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabesa a matsayin jakada a shekarar 2016.

Kara karanta wannan

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: