"PDP Ta Mutu," Kwankwaso Ya Bayyana Jam'iyyar da Ta Ƴunƙuro da Ƙarfinta a Najeriya
- Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce NNPP ta yunƙuro a siyasar Najeriya kuma ta na ƙara samun karɓuwa
- Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 ya ce PDP ta mutu kuma ƴan Najeriya sun gane babu wani alheri a mulkin APC
- Jagoran NNPP na ƙasa ya bayyana haka ne a wurin taron kwamitin zartaswa na ƙasa wanda ya gudana ranar Litinin da ta gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa PDP ta mutu murus a siyasar Najeriya.
Kwankwaso ya kuma caccaki APC bisa nuna halin ko in kula da matsin tattalin arzikin da ƴan Najeriya ke fama da shi, ya ce jam'iyya mai mulki ta gaza.
Tsohon gwamnan ya faɗi hakan ne a wurin taron kwamitin zartaswa na NNPP ta ƙasa wanda ya gudana ranar Litinin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"NNPP ta kere sauran jam'iyyu" - Kwankwaso
Kwankwaso ya ce duk da dimbin kalubalen da jam’iyyar ke fuskanta, NNPP ta kere kowace jam'iyya samun ci gaba a harkokin siyasa a Najeriya.
"Ina farin cikin cewa duk da kalubalen da muke fuskanta, a yau jam’iyyarmu ita ce wadda ta fi kowacce saurin bunƙasa da samun ci gaba a ƙasar nan.
"Ina tuna lokacin da na je Katsina buɗe ofishinmu, na faɗa masu waɗancan jam'iyyun musamman PDP ta mutu, a lokacin da yawa ba su gane ba, amma yau ga shi mu na gani PDP ta rabe gida-gida.
"Wanda bai fahimci bayaninmu a wancan lokacin ba, yanzu ya gane gaskiya muka faɗa, PDP ta mutu."
"APC ta ba mutane kunya" - Kwankwaso
Dangane da APC kuma jagoran NNPP na ƙasa ya ce ƴan Najeriya sun shaida cewa jam'iyya mai mulki ta gaza musamman a ɓangaren tsaro da ƙaruwar talauci.
The Guardian ta ruwaito Kwankwaso na cewa:
"A halin da muke ciki yanzu a mulkin APC, shugabanni suna sama ne ƴan ƙasa kuma muna ƙasa. Ko su yarda ko kar su yarda, ƴan Najeriya da ke ƙaɗa kuri'a sun yi imanin babu wani alheri a tattare da APC.
"Musamman idan muka kalli sha'anin tsaro, ƙaruwar talauci a ƙasa ga kuma uwa uba yunwa da ta yi wa al'umma katutu."
Kwankwaso ya hango nasarar NNPP a 2027
A wani rahoton kuma dan takarar shugaban kasa karkashin NNPP a zaben 2023, Rabiu Kwankwaso ya ce ya hango nasarar jam'iyyar a 2027.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa jam'iyyar NNPP ta yi babban shiri na tunkarar babban zaben 2027 kuma ba za a bar ta a baya ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng