Da duminsa: Jakadan Najeriya a kasar Jordan ya kwanta dama

Da duminsa: Jakadan Najeriya a kasar Jordan ya kwanta dama

- Jakadan Najeriya a kasar Jordan, Haruna Ungogo ya rasu a ranar Lahadi

- Ya rasu ne bayan kwantar da shi asibitin Garki da ke Abuja da kwana biyar

- Majiya daga iyalinsa ta ce za a yi jana'izarsa a ranar Litinin a Kano

Haruna Ungogo, jakadan Najeriya a kasar Jordan, masarautar Hashmite da ke Jordan da Iraq, inda ya rasu yana da shekaru 75 da haihuwa.

Daily Nigerain sun tattaro bayanai a kan mutuwarsa a ranar Lahadi da safe a asibitin Garki da ke Abuja, bayan kwantar da shi da aka yi da kwana biyar.

Majiya daga iyalansa ta ce za a yi jana'izarsa a Kano ranar Litinin.

Yayi aiki da gwamnatin Kano a matsayin sakataren gwamnati, daga baya kuma ya zama shugaban Folitakanik da ke jihar Kano.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabesa a matsayin jakada a shekarar 2016.

KU KARANTA: Ku daina ba mu lambar yabo, kalubalantarmu za ku dinga yi - Wike ga 'yan jaridu

Da duminsa: Jakadan Najeriya a kasar Jordan ya kwanta dama
Da duminsa: Jakadan Najeriya a kasar Jordan ya kwanta dama. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Binciken gida-gida: Shehu Sani ya yi martani mai zafi ga gwamnati

A wani labari na daban, rundunar sojin kasa ta ce ba za ta gabatar da sunayen jami'anta da aka tura Lekki Toll Gate ba, a ranar 20 ga watan Oktoban 2020, The Cable.

Faruwar al'amarin ya janyo hankalin mutanen ciki da wajen Najeriya, yayin da aka zargi sojoji da gwamnatin tarayya da tozarta hakkin bil'adama.

Duk da rahotanni na nuna an kashe mutane da dama, amma har yanzu kisan mutum daya kacal aka tabbatar.

A wata tattaunawa da aka yi da Osoba Olaniyi, kakakin rundunar sojojin 81, sojojin da suka yi aiki a ranar basu amsa sunansu ba.

"Hakan ya ci karo da yadda jami'an tsaro ke gudanar da ayyukansu. A yadda mutane suka yi ta bayar da labarai, kamar muna yakar gwamnati ne, wanda hakan kuskure ne," a yadda jaridar ta wallafa.

Dama rundunar sojojin ta musanta faruwar lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng