A shafa masa lafiya: Alkali ya gargadi EFCC cewa ta kyale Rochas Okorocha ya sha iska

A shafa masa lafiya: Alkali ya gargadi EFCC cewa ta kyale Rochas Okorocha ya sha iska

  • Sanata Rochas Okorocha ya sake kai karar hukumar EFCC a Babban kotun tarayya na garin Fatakwal
  • Tsohon Gwamnan ya koka cewa har yanzu EFCC ta taso shi a gaba duk da hukuncin da aka yi a baya
  • Alkali ya bada umarni a daina binciken Okorocha sai an gama shari’a, amma har gobe ana tuhumarsa

Rivers - Babban kotun tarayya da ke zama a garin Fatakwal, jihar Ribas ta bukaci ta daina duk wani bincike da ta dauko a kan Sanata Rochas Okorocha.

Kamar yadda muka samu labari daga gidan talabijin na Channels TV, kotu ta ce a kyale tsohon gwamnan na Imo har zuwa lokacin da aka gama shari’ar.

Babban lauya Ola Olanipekun (SAN) ya shigar da kara a gaban Mai shari’a Stephen Pam, ya na neman a tursasawa EFCC ta bi umarnin da aka bada a baya.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

A cewar Olanipekun, a Disamban 2021 Alkali ya yanke hukunci cewa a daina binciken Okorocha, kuma ta ce EFCC ta maida masa fasfo da takardun bizansa.

Kamar yadda lauyan ya fadawa kotu a makon nan, EFCC ta ki bin umarnin da aka bada, ta cigaba da binciken da take yi, kuma ta na rike da takardun Okorocha.

Rahoton ya ce lauyan da ya tsayawa Sanatan na Imo ta yamma ya zargi hukumar EFCC da lafto wasu sababbin zargi a kan ‘dan majalisar da yake karewa.

Rochas Okorocha
Sanata Rochas Okorocha Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Da lauyan ya gabatar da kokensa, Mai kare EFCC a kotun tarayyar, N.A. Dodo ya nemi a ba shi lokaci.

N.A. Dodo ya bayyana cewa hukumar EFCC ba ta saba hukuncin da kotun da ke zama a Fatakwal ya yi ba, ya ce an kira Okorocha ya zo ya karbi takardunsa.

Kara karanta wannan

Rikici: APC da Buhari sun nemi a yi watsi da karar da ke neman tsige Buhari a daura Atiku

Lauyan ya ce Sanata Okorocha ne ya ki zuwa ya karbi fasfo da bizarsa. Wannan lamari bai yi wa Stephen Pam dadi, ya ce ba zai bari ayi wasa da shari’a ba.

“Ba na yarda da rashin da’a. Ka da hukumarku tayi wani abu ga wanda ya kawo kara har sai an yanke hukunci. Idan ba ku yarda ba, ku daukaka kara.”

- Alkali Stephen Pam

Okorocha v EFCC

Kafin yanzu lauyoyin Rochas Okorocha sun soma yin galaba a kan hukumar EFCC, aka bukaci a daina bincikensa. Ana zargin EFCC ta bijirewa wannan umarni.

A dalilin haka aka ji Okorocha ya yi zama da shugaba Muhammadu Buhari a Aso Villa. A karshe ya ce shugaban Najeriya ya yarda zai sa baki a wannan maganar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel