Allah ya yiwa uwargidar Sarkin Muradun rasuwa, Buhari ya aika sakon ta'aziyya

Allah ya yiwa uwargidar Sarkin Muradun rasuwa, Buhari ya aika sakon ta'aziyya

Allah ya yiwa Hajiya Rabi Garba, uwargidar Sarkin Murabus a jihar Zamfara, Alhaji Garba Tambari, cikawa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon ta'azziyarsa ga Mai martaba Sarkin ranar Laraba, 9 ga watan Febrairu, 2022.

Mai magana da yawun Shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.

Yace:

"Shugaban kasa a sakon ta'aziyyarsa ga masarautar Muradunya yi addu'an Allah ya jikan marigayiyar wacce ta kasance mutuniyar kirki ga Sarkin fiye da shekaru 40 suna tare."
"Buhari ya yi addu'a ga iyalan Sarkin da al'ummar Maradun, wanda zasu yi matukar rashin Hajiya saboda riko da addininta."

Kara karanta wannan

Buhari ya nufo gida Najeriya bayan kammala taron kungiyar gamayyar kasashen Afrika

Buhari
Allah ya yiwa uwargidar Sarkin Muradun rasuwa, Buhari ya aika sakon ta'aziyya Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel