Sana'a goma: Yadda Dangote ya samu N217.5bn cikin kasa da sa'o'i , ya haura zuwa matsayi na 91 a duniya

Sana'a goma: Yadda Dangote ya samu N217.5bn cikin kasa da sa'o'i , ya haura zuwa matsayi na 91 a duniya

  • Aliko Dangote ya tsallake matsayin attajirai shida a jerin attajiran da suka fi kowa kudi a duniya a jerin da Bloomberg ke bin diddigi
  • Canjin matsayin na Dangote ya biyo bayan karuwar arzikin da ya samu a cikin kwanaki 26 na farkon 2022
  • Arzikin Dangote dai na karuwa ne biyo bayan tashin da aka samu a hannun jarin kamfaninsa na siminti

Attajirin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afrika, Aliko Dangote a cikin sa’o’i 8 da suka gabata, ya samu zunzurutun kudi har Naira biliyan 217.5 ($523M) inda ya zama attajiri na 91 a duniya.

A cewar jeren Bloomberg index, Dangote a yanzu ya haura dala biliyan 20.1 wanda shine 5.23% na ajiyar waje na Najeriya na dala biliyan 40.1.

Kara karanta wannan

Dukiyar sata: Yadda Ministan Buhari ya lallaba, ya ba kamfani kwangilar makudan Biliyoyi

Aliko Dangote, mai kudin Afrika gaba daya
Arziki ya bunkasa: Yadda Dangote ya samu N217.5bn cikin kasa da sa'o'i 8 | Hoto: businessday.ng
Asali: Getty Images

Tashin hannun jarin kamfanin Dangote Cement Plc da kuma jarin mai da takin zamani sun taimaka wajen bunkasar arzikin dan kasuwar dan Najeriya mai shekaru 64.

Tashin arzikin Dangote

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka shi ne ke kula da masana’antar Dangote, kamfaninsa da ke da manyan hannayen jari.

Amma yana samun kari ne a mafi yawan dukiyarsa daga babban kamfanin siminti na Dangote a Nahiyar Afirka.

Hannun jarin kamfanin simintin Dangote a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya a cikin awanni 8 da suka gabata ya haura da 5.45% zuwa N274.8 daga N260 da aka shaida a ranar Laraba.

Dangote ya kuma mallaki fannin sikari, gishiri, mai, taki, da kayan abinci, da kuma gine-ginen gidaje da na kasuwanci guda shida a jihar Legas.

Kara karanta wannan

An kuma: Matashi ya rushe tarihin shekaru 60 a ABU, ya gama da abinda ba'a taba yi ba

Mafi mahimmanci a kadarorinsa, ita ce masana'antar taki da ke iya samar da ton miliyan 2.8 na takin gishiri wato urea a kowace shekara.

Yayin da yake gab da kammala matatar mai mai darajar dala biliyan 19, ana sa ran arzikin Dangote zai kara bunkasa nan da shekaru masu zuwa.

Menene kudin Dangote zai iya saya?

Dala biliyan 20.1 na Dangote na iya siyan tulin oza na zinari miliyan 11.0, da ganga miliyan 219 na danyen mai.

A wani labarin, a shekara ta 11 a jere, hamshakin attajirin nan na Najeriya, Aliko Dangote, ya ci gaba da rike kambin lamba daya a jerin masu tarin kudi a nahiyar Afirka ba tare da fashi ko tsallake ba.

Kamar yadda mujallar Forbes ta fitar a baya-bayan nan, karin 30% na farashin hannun jarin simintin Dangote wanda ya biyo bayan karuwar gine-ginen a Najeriya daga 'yan kasa da gwamnati ya ba da gudummawa ga karin dukiyarsa.

Kara karanta wannan

Duniyar crypto: Yayin da 'yan crypto ke ta kukan faduwa, kamfanin crypto ya tara N13tr

Legit.ng a bincikenta, ta kawo muku wasu sabbin abubuwa guda 4 masu ban sha'awa game da hamshakin attajirin wanda a halin yanzu dukiyarsa ta kai dala biliyan 13.9.

Asali: Legit.ng

Online view pixel