'Yan Boko Haram sun kashe ɗalibai 167 da malaman makaranta 3 a Yobe, Gubana

'Yan Boko Haram sun kashe ɗalibai 167 da malaman makaranta 3 a Yobe, Gubana

  • Gwamnatin Jihar Yobe ta ce mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe dalibai 167 da malamai 3 a jihar
  • Idi Barde Gubana, mataimakin gwamnan Yobe kuma shugaban kwamitin tattara kudade domin tallafawa ilimi ya sanar da hakan
  • Gubana ya shaida wa manema labarai cewa gwamnatin na Yobe ta saka dokar ta baci a bangaren ilimi don farfado da ilimin

Jihar Yobe - Gwamnatin Jihar Yobe ta ce hare-haren yan ta'addar kungiyar Boko Haram ya yi sanadin mutuwar dalibai 167 da malamai uku a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu daliban 86 da malamai biyu sun samu munanan rauni sakamakon hare-haren da yan ta'addan suka kai musu a yunkurinsu na kawo karshen karatun boko a jihar.

'Yan Boko Haram sun kashe ɗalibai 167 da malaman makaranta 3 a Yobe
Boko Haram ta kashe ɗalibai 167 da malaman makaranta 3 a Yobe. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Makashin Hanifa Abubakar: Kotu ta dage zaman hukunta AbdulMalik Tanko

Mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin tattara kudade domin tallafawa ilimi a jihar, Idi Barde Gubana, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi kan rahoton kwamitin.

An saka dokar ta baci a bangaren ilimi a Yobe

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa Gubana ya bayyana cewa kalubalen ne ya janyo gwamnatin jihar ta saka dokar ta baci a bangaren ilimi.

Ya ce an saka dokar ne bayan taro na ilimi da aka yi tare da kafa kwamitin kwararru domin farfado da ilimin firamare da sakandare a jihar.

Ya ce gwamnatin tana kokarin ganin ta inganta ilimi a jihar ta hanyar kara sabbin makaratun frimare da sakandare musamman domin yara mata da mutane masu bukata ta musamman.

A cewarsa, gwamnatin kuma tana da niyyar daukan sabbin malamai, bada horaswa da inganta walwala da jin dadin malamai a jihar.

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.

Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel