Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Isa Borno, Ya Bukaci Sojoji Su Kara Daura Damara

Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Isa Borno, Ya Bukaci Sojoji Su Kara Daura Damara

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira jihar Borno, ya kuma fara yiwa sojoji jawabi
  • Ya bukaci su kara daura damara, domin kuwa akwai manyan ayyuka mai yawa a gabansu
  • Ya kuma ziyarci inda ake jinyar sojojin ya kuma yi tambayoyi tare da sauraran matsalolinsu

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya umarci sojoji da su kara himma a yaki da rashin tsaro "saboda akwai aiki da yawa da za a yi." Daily Trust ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga sojojin rundunar hadin gwiwa a filin Maimalari Cantonment a cikin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Buhari ya isa filin faretin Maimalari daidai karfe 11:30 na safe kuma ya samu tarba daga gamayyar sojoji da ‘yan sanda.

"Bai kamata mu bar abokan gabanmu ko masu aikata laifi su lalata mana ikonmu ba."

KU KARANTA: An kame wani Fasto da ya kashe matarsa, ya binne gawar a kusa da cocinsa

Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Isa Borno, Ya Yi Jawabi Ga Sojoji
Shugaba Muhammadu Buhari a jihar Borno | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

"Yayin da nake yaba muku, bari na fada muku cewa har yanzu akwai sauran aiki a gaba a yankin Arewa maso Gabas, Yamma da kuma kasar baki daya."

Nan take Buhari ya koma inda ake kula da sojojin da suka ji rauni.

Da yake jinjina musu, shugaban ya yi tambayoyi masu yawa.

Tun da farko, a jawabin marabarsa, Mukaddashin Kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai na yaki da tayar da kayar baya, Maj Gen. FO. Omogwui, ya bayyana ziyarar a matsayin "karramawa ta musamman da kuma kara karfin gwiwa" ga sojojin da ke gaba.

Shugaba Buhari zai kaddamar da wasu ayyuka a jihar ta Borno

Hakazalika, rahotan jaridar Guardian ya ruwaito cewa, shugaban kasan za kaddamar wasu ayyuka guda bakwai a jihar ta Borno.

Wasu daga cikin ayyukan da zai kaddamar sun hada da gidaje 4,000 na ‘yan gudun hijirar daga cikin rukunin 10,000 da Gwamnatin Tarayya ke ginawa a Borno da kuma ginin Majalisar Dattawa na Jami’ar Jihar Borno dake birnin Maiduguri.

KU KARANTA: 'Yan Sanda Sun Shiga Shagali Bayan Da ’Yar Sanda Ta Haifi Jarirai ’Yan Uku

Yanzu-Yanzu: Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ya Dira Maiduguri

A wani labarin, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya dira Maiduguri, jihar Borno, a wata ziyarar aiki ta kwana ɗaya da ya kai jihar.

Shugaba Buhari, wanda jirginsa ya dira a filin jirgin ƙasa-da-ƙasa dake Maiduguri da misalin karfe 9:45 na safe, ya samu rakiyar manyan jami'an gwamnatinsa.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, tare da dukan shugabannin jami'n tsaro ƙasar nan ne suka tarbi shugaba Buhari ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel