Gwamnonin Jihohi za su sake sa kafar wando daya da ‘Yan Majalisa kan rigimar dokar zabe

Gwamnonin Jihohi za su sake sa kafar wando daya da ‘Yan Majalisa kan rigimar dokar zabe

  • Akwai yiwuwar sabon rikici ya barke tsakanin Gwamnoni da ‘Yan Majalisa kan dokar zabe ta kasa
  • ‘Yan majalisa sun sake yin wasu kwaskwarima a cikin kudirin zaben da za a kai wa shugaban kasa
  • Gwamnonin jihohi su na tsoron a amince da sharudan da ‘yan majalisa suka zuba a cikin kudirin

Abuja - Za a iya samun sabani tsakanin gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya a dalilin wasu sharudodi biyu da aka cusa a cikin kudirin gyara dokar zabe.

Wani rahoto da Daily Trust ta fitar a ranar Laraba, 2 ga watan Fubrairu 2022 ya bayyana cewa sharudan da aka kawo za su iya sa a kuma yin watsi da kudirin.

A baya shugaba Muhammadu Buhari ya yi fatali da kudirin da ‘yan majalisa suka kawo da yake kokarin yin kwaskwarima ga dokar zaben da ake amfani da ita.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci

Rahoton ya bayyana cewa wannan karo ma gwamnonin za su gwabza da ‘yan majalisar tarayyar wajen ganin shugaban kasa bai rattaba hannu a kan kudirin ba.

Me aka cusa a cikin dokar?

Sashe na 84(9) (a) ya na cewa kafin jam’iyya ta iya tsaida ‘dan takara ta hanyar maslaha, dole sai dukkanin masu neman kujera tare da shi sun nuna janyewarsu.

Dokar ta na so ta wajabta samun takardar janye takara da kuma yi wa wanda jam’iyya ta zaba mubaya’a kafin a iya cewa an fitar da gwani ta hanyar maslaha.

‘Yan Majalisa
'Yan majalisar wakilan tarayya Hoto: HouseNGR
Asali: Facebook

Idan ba a samu wannan ba, dole sai an yi zaben fitar da gwani kafin a iya tsaida ‘dan takara.

Wani sashe da aka shigo da shi a kudirin gyaran zaben yana so duk wadanda suke rike da mukami a matakin jiha da tarayya su yi murabus kafin su shiga zabe.

Kara karanta wannan

Matan APC sun fadakar da Duniya kan shirin wasu Gwamnonin Arewa 3 na rusa Jam’iyya

Wata majiya ta bayyana cewa wasu daga cikin gwamnoni ba su yarda da wadannan kare-kare da ake neman ayi wa dokar zaben ba, su na ganin ana neman karya su.

Gwamnoni da Ministoci za su yaki wadannan sharudan biyu da majalisa ta ke son kawowa na tursasa ajiye mukamai kafin a shiga zabe da batun tsaida ‘dan takara.

Yusuf Baba Ahmed zai nemi gwamna

Tsohon ‘Dan Majalisar Zaria da ya taba takarar shugaban kasa ya ce zai nemi gwamna a Kaduna. Yusuf Baba Ahmed ya ce kishi da kokarin kawo gyara ya sa zai yi takara.

Shugaban jami’ar ta Baze University ya taba lashe zaben Majalisar tarayya sau biyu a ANPP da CPC, kafin ya yi watsi da APC, ya bi PDP da ya nemi ta ba shi takara a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel