Dillalin gidaje ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matar aure

Dillalin gidaje ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matar aure

Ogun - Wani dillalin gidaje, Diran Elijah, ya rasa rayuwarsa bayan jima'i da tsohuwar matarsa mai suna Idowu, a wani da dakin Otal dake unguwar Agbado a jihar Ogun.

Idowu da Elijah sun rabu shekaru hudu da suka gabata kuma dukkansu sun sake wani aure.

Idowu ta haifawa sabon mijinta yara biyu amma ta fita kwanciya da tsohon mijin.

Jihar Ogun
Dillalin gidaje ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matar aure Hoto: Jihar Ogun
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

City Round ta ruwaito cewa sun hadu a Otal ne bayan Elijah ya kirata a waya domin sun hadu misalin karfe 10 na dare ranar Lahadi.

Bayan jami'in da suka yi, sai mutumin ya kwanta don hutawa kawai sai ya yanke jiki.

Kara karanta wannan

Takarar Atiku na rawa: Jagoran kamfen dinsa a arewa maso gabas da sauransu sun koma tsagin APC

Kafin matar ta janyo hankali masu Otal din Elijah ya mutu.

Wani mazaunin unguwar masi suna Afolabi ya bayyanacewa jaridar Punch cewa wannan abu ya tada hankalin al'ummar unguwar yayinda yan sanda suka dira gudanar da bincike.

Yace:

"Mai Otal din ya so yin karya cewa mutumin a waje ya fadi ya mutu. Amma matar (Idowu) tace karya ne, sun yi jima'i ne kuma yace bari ya huta amma bai tashi ba. Bayan yan mintuna kadai sai numfashinsa ya dauke."
"Ta kira ma'aikatan Otal din amma tuni ya kwanta dama. Daga baya na samu labarin sun taba aure amma suka rabu."

Wata majiya ta bayyana cewa matar ta karbi bashi ne amma ta gaza biya, sai Elijah yayi alkawarin bata kudi don ta biya bashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: