Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kai sabon hari, sun sace mutane kusan 60 a Katsina

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kai sabon hari, sun sace mutane kusan 60 a Katsina

  • Wasu bindiga sun sake kai mummunan hari jihgar Katsina, sun yi barna mai yawa da sace dunkiyoyi
  • Sun kuma sace mutane sama da 50 a wani yankin yayin da suka zo a kan babura sama da 60, inji majiyoyi
  • An ce akwai sojoji a yankin, amma basu iya kawo wa mazauna yankin dauki ba har sai bayan da aka gama barnar

Jihar Katsina - Rahoton Daily Trust ya ce, sama da mutane 50 ne aka sace a kauyen Ruwan Godiya da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina a wani sabon hari da aka kai, kamar yadda majiya ta bayyana.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun zo ne a kan babura sama da 60 kuma suka fara harbe-harben iska.

Kara karanta wannan

Basarake da 'yan tawagarsa na asibiti rai a hannun Allah bayan harin da aka kai masa

'Yan bindiga a Katsina
Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kai sabon hari, sun sace mutane kusan 60 a Katsina | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya ce sun shafe sama da sa’o’i biyu suna gudanar da barnar ba tare da wani kalubale ba.

Mazaunin garin ya shaida cewa akwai sojoji sama da 20 a kauyen a lokacin da lamarin ya faru amma ba su yi wani yunkurin dakile harin ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Tun kafin su zo mun samu labarin shirinsu na kai farmaki kuma mun sanar da jami’an tsaro, amma abin takaici sai suka zo da misalin karfe 7:30 na dare kuma sun shafe sama da sa’o’i biyu a garin.
“Sun raunata mutane uku amma babu wanda ya mutu. Sai dai sun yi awon gaba da mutane sama da 50 bayan sun yi awon gaba da wasu kayayyaki masu daraja da suka hada da kayan sawa."

Wani mazaunin garin ya yi zargin cewa sojoji da suka fito daga bangaren Sheme na karamar hukumar sun ga maharan sun tsallaka kan hanya tare da mutanen da aka yi garkuwa da su, amma ba su yi wani yunkurin kubutar da su ba.

Kara karanta wannan

Niger: Rayuka birjik sun salwanta, gidaje sun babbake a sabon harin ƴan ta'adda

Hare-haren baya-bayan nan

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kasuwar Yandaka da ke karamar hukumar Batsari inda aka ce sun yi awon gaba da duk wasu dabbobin gida da aka kawo kasuwa domin sayarwa.

A ranar Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka kai wani kazamin hari a kauyen Illela da kewaye, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 12.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Sarkin Katsina ya shaida wa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo cewa shi da Gwamna Bello Masari ba sa iya bacci saboda matsalar rashin tsaro, inda ya nemi a hallaka duk dan bindigan da aka kama

A wani labarin, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, an kama wani likita da ake zargin ya yi jinyar harbin bindiga ga dan ta'adda Bello Turji a jihar Sokoto.

An kama likitan mai suna Abubakar Kamarawa ne a wani gagarumin samame da jami’an tsaro suka kai kan 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Niger: Ƴan ta'addan sun kai sabon hari, sun sheƙe rai 2, sun sace sama da mutum 100

An kama shi ne tare da wasu 'yan ta'addan a wasu ayyuka daban-daban a fadin kananan hukumomi uku na jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.