Da Dumi-Dumi: Tanka Makare da Man Fetur Ta Yi Bindiga a Tsakiyar Shagunan Mutane

Da Dumi-Dumi: Tanka Makare da Man Fetur Ta Yi Bindiga a Tsakiyar Shagunan Mutane

  • Wata tankar dakon man fetur ta fashe ta kama da wuta a wurin dake tara cunkoson ababen hawa a birnin Onitsha, jihar Anambra
  • Rahoto ya bayyana cewa wutar ta cinye shaguna da gine-ginen dake kusa da wurin da lamarin ya faru
  • Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar yace tuni jami'an yan sanda da na hukumar kwana-kwana suka kai ɗauki

Anambra - Wata Tanka maƙare da man fetur ta fashe da safiyar Jumu'a a mahaɗar hanyoyi ta Upper Iweka Onitsha, jihar Anambra.

Punch ta rahoto cewa ana tsammanin duk shagunan da ginin dake wurin sun kone sakamakon wutar da ta kama bayan fashewar Tankar a hanya mai tattara mutane Onitsha-Owerri.

Wutar ta fara ci ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe kuma ta haddasa cinkoson ababen hawa a ciki da wajen birnin Onitsha.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Tanka ta kama da wuta
Da Dumi-Dumi: Tanka Makare da Man Fetur Ta Yi Bindiga a Tsakiyar Shagunan Mutane Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A halin yanzun jami'an hukumar kwana-kwana na jihohin Anambra da Delta, sun dira wurin, yayin da suke kokarin kashe wutar duk da ƙarancin ruwan da ake fama da shi.

Meya haddasa lamarin?

Wani shaidan gani da ido ya bayyana wa wakilan mu cewa wata babbar motar dakon kaya ce ta haddasa fashewar Tankar, bayan ta faɗi a kan hanyar Onitsha-Owerri.

Kakakin yan sanda reshen jihar, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

The Nation ta rahoto Kakakin yan sandan ya ce:

"Bayanan da muka samu sun nuna cewa wutar ta kama ne sakamakon wata Tankar dakon man Fetur da ta faɗi a Obodoukwu junction, kan hanyar Onitsha zuwa Owerri."
"Lamarin na karkashin kulawar mu kuma idon mu na kai. A halin yanzun yan sanda da jami'an kashe wuta suna wurin."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba da ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa a Najeriya

A wani labarin kuma Cikin jihohi 36, An bayyana gwamnan jihar da ya fi kaunar zaman lafiya a Najeriya

Gidauniyar wanzar da zaman lafiya ta baiwa gwamnan jihar Enugu, lambar yabo ta gwamnan da ya fi son zaman lafiya a Najeriya.

Shugaban gidauniyar, Dakta Sulaiman Adejoh, yace sun yi nazari kan muhimman ayyukan gwamnan kafin su zaɓe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel