Samun man fetur ya yi wahala, jama'a sun koka, sun ce za su fara zanga-zanga

Samun man fetur ya yi wahala, jama'a sun koka, sun ce za su fara zanga-zanga

  • Mazauna Saki a jihar Oyo sun koka kan yadda farashin man fetur ya zama abin damuwa ga mazauna yankin
  • 'Yan yankin sun koka kan yadda gidajen mai suke daukar man fetur zuwa jamhuriyar Benin a cikin wannan lokaci na matsi
  • Sun ce nan ba da jimawa za su tsunduma zanga-zanga idan gwamnatin Buhari bata duba ta dauki mataki ba

Saki, Oyo - Al’ummar garin Saki da ke yankin Oke-Ogun a jihar Oyo a ranar Alhamis din da ta gabata sun yi barazanar fara zanga-zangar nuna rashin amincewa da karanci da karin farashin man fetur a yankin.

Sun bayyana fasakwaurin mai da ake yi daga Najeriya zuwa jamhuriyar Benin a matsayin abin da ya janyo karancin man, inda suka shawarci gwamnati da ta magance matsalar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Idan kuka kara farashin mai, zaku sake jefa miliyoyin mutane talauci: Janar AbdulSalam

Man fetur ya yi wahala, 'yan kasa sun shiga damuwa
Samun man fetur ya yi wahala, jama'a sun koka, sun ce za su fara zanga-zanga | Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Saki gari ne mai iyaka da Najeriya da Jamhuriyar Benin.

Shugaban kungiyar Saki First, wata kungiyar al’adu a garin, Mista Lawal kunle, wanda ya tabbatar da karancin mai ga manema labarai a Ibadan, ya ce karin ya shafi dukkan harkokin kasuwanci a yankin.

Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya ido a kan harkokin dillalan man fetur a yankin domin ganin rayuwa ta yi wa al’ummar Saki kunci a yanzu.

Wani mazaunin garin na Saki da ya nemi a sakaya sunansa ya ce da yawa daga cikin ‘yan kasuwar man fetur na safarar kayan ne daga cikin kasar a yayin da mutanen Saki ke shan wahala.

A cewarsa:

“Idan farashin man fetur ya tashi kuma muna samun shi cikin sauki, ba za mu sami wata matsala ba amma matsalar ita ce ba ma samunsa da sauki. Babu gidan mai da ke sayar da mai a Saki kamar yadda muke magana yanzu.

Kara karanta wannan

Watan Yuni zamu yanke shawara kan kara farashin litan man fetur, Majalisar tattalin arzikin Najeriya

“Abin takaici, masu tuka babura sun kara kudin da kusan 100%. Ko da ruwan fiya wata ana sayar da shi akan N15 a Saki. Yanzu dai kowa na DAURA hauhawar farashin kayan masarufi akan man fetur. Ba za mu iya ci gaba a haka ba."

Kokarin jin martanin hukumar kula da albarkatun man fetur (DPR) a jihar ya ci tura domin an kira wayar shugabanta, Niyi Olowokekere amma a kashe kuma bai amsa sakon tes da aka aika masa ba.

Buhari yace min bai sa kowa kara farashin man fetur ba: Shugaban majalisa

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai ba kowa umurnin kara farashin man fetur ta hanyar cire tallafin gwamnati ba.

Ahmad Lawan ya bayyana hakan ne yayin hirarsa da manema labarai bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ranar Talata, 18 ga Junairu, 2022, rahoton DailyTrust.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi shigar soji, sun dauke ‘yan biki, sun bukaci a biya fansar Naira Miliyan 60

Yace yana farin cikin fadawa yan Najeriya cewa Buhari bai sa kowa cire tallafin mai ba.

Zaku tuna cewa a watan Oktoba, Ministar kudi, Hajiya Zainab Ahmed ta sanar da cewa gwamnatin tarayya zata cire tallafin mai bayan rabin shekarar 2022.

A cewarta, za'a baiwa talakawan Najeriya milyan arba'in kudi dubu biyar-biyar matsayin kudin mota don rage radadin karin da farashin man zai yi.

A baya kunji cewa, Kungiyar Kwadagon Najeriya NLC, ta lashi takobin cewa yan Najeriya ba zasu yarda da wani sabon karin farashin man fetur ma da sunan cire tallafin mai.

NLC ta yi kira ga ma'aikata da yan Najeriya su shirya zanga-zanga kan wannan abu da gwamnati ke shirin yi.

Shugaban NLC, Ayuba Wabbab, ya bayyana hakan a jawabin sabon shekara da ya saki ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.