Allah ya yiwa mahaifiyar attajiri Dahiru Mangal, rasuwa

Allah ya yiwa mahaifiyar attajiri Dahiru Mangal, rasuwa

Allah ya yiwa Hajiya Murja Mangal, mahaifiyar shahrarren attajiri dan jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal, rasuwa.

Hajiya Murja ta mutu ne a daren Alhamis tana mai shekaru tamanin da biyar (85) bayan gajeruwar jinya.

Majiyar Vanguard ta ce za'a gudanar da jana'izah bayan Sallar Juma'a yau 21 ga watan Junairu, 2022.

Alhaji Dahiru Barau Mangal ne mammalakin kamfanin Afdin Group, kamfanin jirgin Max Air, dss.

Allah ya yiwa mahaifiyar attajiri Dahiru Mangal, rasuwa
Allah ya yiwa mahaifiyar attajiri Dahiru Mangal, rasuwa
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel