Yanzu-yanzu: Gobara ta kashe mutum 14 a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

Yanzu-yanzu: Gobara ta kashe mutum 14 a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

- Mutum 14 ne suka rasa rayukansu a sansanin 'yan gudun hijira da ke karamar hukumar Ngala da ke jihar Borno

- A jiya ranar Alhamis ne gobara ta barke a sansanin 'yan gudun hijira da wajen karfe 2:15 na rana

- Mutum 7 sun samu miyagun raunika inda mutum 8 suka samu kanana raunika

'Yan gudun hijira 14 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da 15 daga ciki suka samu raunika daban-daban.

Hakan ya faru ne sakamakon barkewar gobara a sansanin 'yan gudun hijarar da ke karamar hukumar Ngala ta jihar Borno.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, gobarar ta fara ne da karfe 2:15 na yammacin ranar Alhamis a sansanin.

Kamar yadda wata majiya ta tabbatar, an yi kokari wajen kashe wutar da gaggawa.

"A halin yanzu, ranar 16 ga watan Afirilun 2020, gobara ta kama a sansanin 'yan dudun hijira da ke Ngala. Gobarar ta lashe gidaje 1250 amma ba a tabbatar ba," majiyar ta ce.

Yanzu-yanzu: Gobara ta lashe rayuka 14 a sansanin 'yan gudun hijira a Borno
Yanzu-yanzu: Gobara ta lashe rayuka 14 a sansanin 'yan gudun hijira a Borno
Asali: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Hotunan yadda dan kamfai na mata ya zama takunkumin rufe fuska a Kenya

Ta kara da bayyana cewa, "Mutum 14 ne suka rasa rayukansu, mutum 7 sun samu miyagun raunika yayin da mutum 8 suka samu kananan rauni".

A lokacin da majiyar ke sanarwa, ana ci gaba da kwashe mutane tare da kayayyakinsu da ke sansanin.

A wani labari na daban, The Punch ta ruwaito cewa ba a san ainihin abinda ya yi sanadin gobarar da ta kone shaguna masu lamba 35 da 36 a kasuwar a lokacin da ake rubuta wannan rahoton.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu ya ce masu kai tallafin gaggawa sun ci karfin wutar kuma babu wanda ya rasa ransa sakamakon gobarar.

Ya ce, "Da isar masu taimakon gaggawar, an gano cewa wutar ya tashi ne daga wani rukununin shaguna ta Maola Shopping Mall amma ba'a gano abinda ya yi sanadin gobarar ba.

"Jami'an LASEMA daga yankin Legas ta tsakiya (Sari Iganmu) da jami'an hukumar kashe gobara da 'yan sanda sun yi nasarar kashe gobarar kuma saman ginin ne shaguna masu lamba 35 da 36 ne gobarar ta shafa.

"Masu taimakon gaggawa sun kashe wutar sun koma ofishinsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: