Sani Bello: An fuskanci Farmaki 50, asarar rayuka 220 a Niger cikin watan Janairu

Sani Bello: An fuskanci Farmaki 50, asarar rayuka 220 a Niger cikin watan Janairu

  • Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya ce a kalla fararen hula 165, jami’an tsaro 25 da kuma ‘yan Sa Kai 30 sun rasa rayukansu cikin kwana 17 na farkon shekarar nan
  • Gwamnan ya bayyana wannan yawan ne bayan kammala wani taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja a ranar Talata
  • Kamar yadda ya shaida, an kai hare-hare 50 a jihar sa yayin da suka afka anguwanni a kalla 300 tare da sace mutane 200 duk da ‘yan China tsakanin 1 zuwa 17 ga watan Janairu

Niger - Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya bayyana yadda a kalla fararen hula 165, jami’an tsaro 25 da ‘yan Sa Kai 30 suka rasa rayukan su cikin kwanaki 17 na farkon shekarar nan.

Kara karanta wannan

An kuma: An sake yin garkuwa da wani basaraken gargajiya a jihar Filato

Gwamnan ya sanar da wannan yawan ne bayan kammala taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja a ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Sani Bello: An fuskanci Farmaki 50, asarar rayuka 220 a Niger cikin watan Janairu
Sani Bello: An fuskanci Farmaki 50, asarar rayuka 220 a Niger cikin watan Janairu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A cewar sa, ‘yan ta’adda sun kai farmaki 50 a jihar sa wanda ya janyo rashe-rashen rayuka tsakanin ranar 1 ga watan Janairu zuwa 17 yayin da suka afka garuruwa 300 cikin lokacin, inda suka yi garkuwa da mutane 200 ciki har da ‘yan China.

Sai dai ya bayyana fatan sa a kan jihar za ta samu ingantaccen tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

A ranar Lahadi shugaban kasa ya umarci sojoji su tabbatar sun dauki tsattsauran mataki akan kashe-kashe da garkuwa da mutanen jihar Neja.

Kamar yadda gwamnan yace:

“Da ranar nan, na kawo wa shugaban kasa ziyara don sanar da shi abinda ake ciki dangane da ta’addanci, garkuwa da mutane da satar shanu a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

“Mun samu damar tattaunawa kwarai da shi. Mun zanta dangane da wasu hare-hare na jihar. Sai dai ba zan iya bayyana muku duka ba. A ‘yan kwanakin nan abubuwa da dama sun faru a jihar Neja amma muna sa ran za a samu sassauci dangane da rashin tsaron.
“Ya kuma ba mu mafita a kan matsalolin tsaro. Girman jihar ya na ba mu matsala, a kalla mun kai hectare miliyan 9. Mun rasa wasu dazukan.
“A watan Janairu kadai, mun samu rahotanni a kan hare-hare 50 wadanda aka rasa rayuka sanadin shi. Cikin dan datsin, ‘yan bindiga sun shiga fiye da garuruwa 300. An yi garkuwa da mutane 200 ciki har da ‘yan China 200. Mun rasa jami’an tsaro 25. Sannan mun rasa fararen hula 165 da ‘yan sa kai 30. Abinda muke ta fama da shi kenan tun farkon shekarar nan.
“Amma ga jajircewar da jami’an tsaron mu suke yi, na san za a samu mafita cikin gaggawa. Kuma cikin dan kankanin lokaci za a samu sauki da zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya ba sojoji umurnin yin gaggarumin aiki a wata jihar Arewa

“Amma duk da haka muna da aiki tukuru a gaban mu. Muna da iyaka da Kaduna, Zamfara da jihar Kebbi. Kuma ‘yan bindiga suna shiga dajika daga Zamfara zuwa Kebbi da kuma Kebbi zuwa Neja. Suna amfani da damar kiwon shanu su sace shanun jama’a sannan suna yawo a babura. Kuma duk garuruwan da suke kai hari ba su da titina don haka ba za mu iya isa wurin da gaggawa ba.
“Ba ma jin dadin abinda ke faruwa da jihar nan. Kuma muna iyakar kokarin mu wurin ganin mun kawo karshen shi.”

‘Yan bindiga sun yi shigar soji, sun dauke ‘yan biki, sun bukaci a biya fansar Naira Miliyan 60

A wani labari na daban, wasu ‘yan iskan gari da suka yi shiga tamkar jami’an sojojin kasa, sun dauke mutane bakwai da ke dawowa daga bikin daurin aure a Isara, jihar Ogun.

Jaridar Punch ta ce an dauke wadannan Bayin Allah ne a kan hanyar Legas zuwa garin Ibadan.

Kara karanta wannan

Ta’addanci: Masu kai wa 'yan bindiga bayanai sune babbar matsalar mu, El Rufai

Rahoton ya ce mutanen da aka sace su na hanyar dawowa gida ne daga wajen biki da aka yi a garin Ibadan, jihar Oyo a ranar Asabar, 16 ga watan Junairu, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng