Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 15 a wani hari da suka kai jihar Neja
- Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 15 a wani farmaki da suka kai kauyen Kulho a karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja
- Kakakin rundunar yan sandan jihar Wasiu Abiodun, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu
- Ya ce an tura jami'an rundunar domin gudanar da aikin bincike da ceto mutanen
Niger - A kalla mutane 15 aka yi garkuwa da su bayan wani hari da yan bindiga suka kai kan al'umman wani gari a jihar Neja.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu.
A cewar Abiodun, yan bindigar sun farmaki Kulho, wani kauye da ke kusa da yankin Ibbi a karamar hukumar Mashegu sannan suka yi garkuwa da mutane 15 a ranar 14 ga watan Janairu.
Ya ce maharan sun kuma farmaki Mashegu ta jihar Jigawa sannan suka yi awon gaba da wasu dabbobi da ba a tantance adadinsu ba a wannan rana.
A cewarsa, an zuba jami'an tsaro domin su gudanar da shirin bincike da kuma ceto wadanda lamarin ya ritsa da su, rahoton Premium Times.
Ya ce:
"Mun nemi taimakon mazauna yankin da su bayar da gudummawar ingantattun bayanai da za su taimaka wajen kama miyagun."
Buhari ya ba sojoji umurnin yin gaggarumin aiki a wata jihar Arewa
Ahalin da ake ciki, mun kawo a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci rundunar soji da dauki gagarumin mataki kan lamarin kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Neja.
The Nation ta rahoto cewa Buhari ya kuma umurci sojojin da su yi amfani da karfi a tsarin kakkabe yan ta'ddan da suka addabi jihar.
Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin labarai, Garba Shehu, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu, ya ce shugaban kasar ya bayar da umurnin ne ga hedkwatar tsaro, rahoton Daily Trust.
Asali: Legit.ng