Zamfarawa sun yi zanga-zanga saboda tsanantar kashe-kashe a yankunan su
- Jama'ar Nahuche da ke karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara a ranar Lahadi sun fita zanga-zanga har gaban gidan gwamnatin jihar
- Suna bukatar gwamnati da ta tsananta tsaro a yankin saboda yadda 'yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka ta hanyar kashe su ko da sun biya kudin fansa
- Tsohon shugaban karamar hukumar ya sanar da yadda 'yan ta'addan suke addabarsu, a halin yanzu akwai mutum 13 na yankin a hannun miyagun
Bungudu, Zamfara - Mazauna yankin Nahuche da ke karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara a ranar Lahadi sun yi zanga-zangar lumana a Gusau inda suka bukaci hukumomi da su tsananta tsaro a yankin kan kisan gillar da 'yan ta'adda ke yi musu.
Masu zanga-zangar wadanda suka garzaya gidan gmwamnatin jihar sun samu jagorancin tsohon shugaban karamar hukumar Bugudu, Musa Abdullahi Manager.
Ya ce ana kai musu farmaki a kowacce rana kuma ana sace jama'a inda ake karbar kudin fansa, hakan kuwa ba adalci ba ne, Daily Trust ta ruwaito.
"A shekaru uku da suka gabata, yankin mu ya fuskanci farmaki kusan 12 inda aka kashe mutane ko kuma aka yi garkuwa da su tare da karbar kudin fansa da zai kai miliyan dari da kuma kudin 'yan banga, amma komai cigaba ya ke.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“'Yan ta'adda sun kutsa yankin tare da sace mutane kuma an biya su N5 miliyan amma sun ki sakin su, a maimakon hakan sai suka bukaci babura sabbi guda biyu.
"A yayin da ake wannan cinikin, 'yan ta'addan sun dawo tare da kara satar mutane takwas kuma har yanzu ba su bukaci kudin fansa ba.
“Mu na da kusan mutum 13 da ke hannun 'yan ta'adda kuma muna kira ga hukumomi da su ceto su," yace.
Ya yi bayanin cewa, wani dan kasuwa mai suna Alhaji Hadi Babban Gebe an sace shi cikin kwanakin nan kuma 'yan ta'addan sun bukaci kudin fansa har N35 miliyan.
Ya kara da cewa, sun kashe dan kaswaur kuma suka karbe kudin fansar, Daily Trust ta ruwaito.
"Mutane masu tarin yawa sun bar yankin saboda hare-haren sun ki ci balle cinyewa duk da suna biyan kudi mai yawa ga 'yan banga domin ba su kariya.
“Muna bukatar a tura mana jami'an tsaron dindindin a yankin. Mun san gwamnatin jiha da ta tarayya ta na kokari, amma a gaskiya halin da Nahuche ke ciki, akwai bukatar taimakon gaggawa ko kuma wurin zai koma kufai nan gaba," ya ja kunne.
An kasa samun kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, kafin rubuta wannan rahoton domin tsokaci.
Zamfara: 'Yan daban siyasa sun lakada wa mai sukar Matawalle duka, sun farfashe motarsa
A wani labari na daban, makonni biyu bayan kai farmaki ofishin wata jaridar yanar gizo da gidan talabijin, wasu da ake zargin 'yan daban siyasa ne a ranar Juma'a sun kai mummunan farmaki kan mai sukar Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara inda suka ragargaza motarsa a Gusau.
An lakada wa Shamsu Kasida mugun duka kuma an farfasa motarsa yayin da ya tsaya a wani wurin cin abinci da ke kusa da gidan gwamnatin jihar a Gusau, Premium Times ta ruwaito.
Manajan daraktan gidan talabijin na Thunder Blowers, Anas Anka, ya zargi gwamnan jihar da daukar nauyin farmakin farko. Ya ce a tuhumi gwamnan a duk lokacin da mummunan lamari ya faru da shi ko ma'aikacinsa.
Asali: Legit.ng