Duniya kenan: Matashi ya yi garkuwa da yarinya 'yar shekaru 13, ya yanka ta sannan ya nemi kudin fansa a Kano

Duniya kenan: Matashi ya yi garkuwa da yarinya 'yar shekaru 13, ya yanka ta sannan ya nemi kudin fansa a Kano

  • Rundunar yan sandan jihar Kano sun damke wani matashi mai shekaru 21, Auwal Abdulrasheed, bisa garkuwa da wata yar talla
  • Abdulrasheed dai ya sace yarinyar, ya yanka ta sannan kuma ya nemi kudin fansa daga wajen yan uwanta
  • Kakakin yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da lamarin inda yace za a mika matashin kotu don yanke masa hukunci

Kano - Wani matashi mai shekaru 21, Auwal Abdulrasheed wanda yan sandan jihar Kano suka kama ya yi bayanin yadda yayi garkuwa da wata yar talla mai shekaru 13.

Ya kuma yi bayanin yadda ya kashe ta sannan ya nemi yan uwanta su biya kudin fansa naira miliyan daya bayan ya binne gawarta a rami mai zurfi, shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan daba sun wanke jigon APC da wasu mutane da ruwan 'Acid' a Adamawa

Duniya kenan: Matashi ya yi garkuwa da yarinya 'yar shekaru 13, ya yanka ta sannan ya nemi kudin fansa a Kano
Duniya kenan: Matashi ya yi garkuwa da yarinya 'yar shekaru 13, ya yanka ta sannan ya nemi kudin fansa a Kano Hoto: Daily Trust

Kakakin yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 11 ga watan Janairu, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 9 ga watan Janairu.

Yadda lamarin ya faru

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa a ranar 21 ga watan Yuli, 2021, an kai rahoton batar wata yarinya yar shekara 13 mai suna Zuwaira ofishin yan sanda.

“A ranar 21/06/2021 da misalin karfe 1000, an samu rahoto daga wani mazaunin garin Tofa, karamar hukumar Tofa, jihar Kano cewa an yi garkuwa da yarsa Zuwaira mai shekaru 13 kuma an nemi kudin fansa naira miliyan daya sannan daga bisani aka daidaita kan N400,000. Yayin da ake tattauna batun kudin fansar, sai aka gano gawar yarinyar a wani kango an yanka ta sannan aka binne ta.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

“Da aka samu rahoton mummunan lamarin, sai aka ziyarci wajen, aka ciro gawar, likitoci suka gwada sannan suka tabbatar da mutuwarta inda aka mika ta ga yan uwanta don binneta daidai da koyarwar musulunci.
“Nan take sai kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Samai’ila Shuaibu Dikko, ya umurci wata tawaga karkashin jagorancin SP Shehu Dahiru da su kamo masu laifin.
“Rundunar yan Puff Adder suka shiga bincike. Kokari da ake tayi da bibiyar lamarin ya kai ga kama wani Auwalu Abdulrashid da aka fi sani da Lauje mai shekaru 21 a garin Tofa, karamar hukumar Tofa, jihar Kano a kauyen Dan Marka, karamar hukumar Dambatta, jihar Kano a ranar 09/01/22 wato kwanaki 202 bayan faruwar lamarin.
“A binciken farko, wanda ake zargin ya tona cewa shi kadai yayi garkuwa da yarinyar, ya yaudareta Sannan ya kaita wani kango a garin Tofa, karamar hukumar Tofa, jihar Kano, inda ya makureta da Hijabinta yayi amfani da wuka wajen yanka mata wuta Sannan ya binne ta a rami, sai kuma ya nemi kudin fansa naira miliyan daya amma daga baya suka tsaya kan N400,000.

Kara karanta wannan

Direban NAPEP ya shiga hannu yayin da ya yi garkuwa da kansa, ya nemi kudin fansa

“Wanda ake zargin ya ci gaba da tona cewa a ranar 07/06/2021, ya yi garkuwa da kanin yarinyar, wani Muttaka mai shekaru uku a garin Tofa sannan ya nemi a biya naira miliyan 2 kudin fansa, daga bisani suka sasanta ya karbi N100,000 inda ya yasar da shi a makarantar Firamare ta Dawanau, karamar hukumar Dawakin Tofa, jihar Kano.”

Rundunar yan sanda ta kammala bincike

Kakakin ya kuma bayyana cewa yan sanda sun kammala bincike kan lamarin, ya ce za a mika wanda ake zargin kotu don yanke masa hukunci, rahoton PM News.

Ci da ceto: Duk da yaye rufin gidansa domin ya biya kudin fansa, wasu na kokarin damfarar dattijo

A wani labarin kuma, mun ji cewa mutumin Katsinar nan da ya yaye rufin kwanon gidansa domin ya siyar saboda ya ceto yaronsa daga hannun masu garkuwa da mutane ya ce wasu mutane sun mayar da halin da yake ciki harkar kasuwanci.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

Saidu Faskari ya yaba ma yan Najeriya da suka kawo masa dauki bayan an wallafa labarinsa, amma ya ce mutane su daina aika kudi da sunansa saboda ‘an cimma adadin kudin da ake so’, Premium Times ta rahoto.

Ya yi magana ne ta hannun makwabcinsa, Ibrahim Bawa, wanda yake ta karbar gudunmawa a madadinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng