Shehu Sani: 'Yan bindiga sun zama jiha mai zaman kanta a cikin jihohin Arewa maso Yamma
- Sanata Shehu Sani ya magantu a kan matsalar rashin tsaro da ya addabi jihohin arewa
- Sani ya ce yan bindiga a yankin arewa maso yamma sun kafa gwamnati inda suka nada hakimai da limamai
- Sani ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya kira tsoffin abokai da makwabtansa na Katsina domin jin halin da ake ciki
Kaduna - Tsohon dan majalisar dattawa da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya ce yan bindiga sun zama jiha mai zaman kanta a cikin jiha a yankin arewa maso yamma.
Sani ya koka ne a yayin wata hira a shirin gidan talbijin na Channels a ranar Talata, 11 ga watan Janairu.
Ya ce:
“Kusan a yanzu, yan bindiga a Arewa maso yamma sun zama jiha mai zaman kanta a cikin jiha.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Sun yi nasarar kafa tsarin gwamnati ta yadda ba wai kawai suna garkuwa da mutane da karbar kudi bane, ta kai har suna nade-nade.
“A cewar rahotanni, sun kafa sarakunan gargajiya da limamai.”
Yan bindiga na ci gaba da kai munanan hare-hare a Kaduna, Zamfara, Sokoto, Katsina, da Neja a jihohin arewa, inda suke kashewa tare da garkuwa da daruruwan mutane.
Da yake bukatar hukumomi da su kara kokarinsu kan miyagu, Sanata Sani ya yarda cewa ya kamata gwamnati ta kara kaimi don tsaron rayuka da dukiyoyin mutane.
Ya ci gaba da cewa:
“Ba wai a duniyar taurari wannan ke faruwa ba, hakan na faruwa ne a jihar shugaban kasa (Katsina).
“Yan bindiga sun zama hukuma - suna kashe wadanda suka ga dama, suna kyale wadanda suka ga damar kyalewa.
“A jihohin Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi, Sokoto da Neja, wurare da dama na a karkashin kulawar wadannan yan bindiga.”
Ya ce, hare-haren kwanan da aka kai kauyuka da dama a Zamfara martani ne ga yakin da sojoji suka kaddamar kan yan bindigar.
Abun da ya kamata Shugaba Buhari yayi a yanzu
Rahoton ya kuma kawo cewa Sani ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kira tsoffin abokai da makwabtansa don samun bayanai kan halin da ake ciki.
Ya ce:
“Ya kamata shugaba Buhari ya ware lokaci, ya duba tsohuwar takardarsa, ya duba lambobin wadannan tsoffin abokan nasa da mutanen da ya daina hulda da su tun shekaru hudu zuwa bakwai da suka gabata, ya kira su sannan ya tambayi abun da ke faruwa.”
Kashe-kashen jihar Zamfara ba zai tafi a banza ba, in ji APC
A wani labarin, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta bayyana cewa kashe-kashen da ake aikatawa mutane a jihar Zamfara ba zai tafi a banza ba tare da hukunci ba, jaridar The Cable ta rahoto.
Hakan martani ne ga kisan kiyashin da yan bindigar da ke tserewa harin sojoji suka yi wa mutane musamman mata da kananan yara.
Har yanzu dai akwai sarkakiya kan yawan mutanen da aka kashe a harin, yayin da gwamnatin jihar ta yi ikirarin cewa kimanin mutane 58 aka kashe.
Sai dai kuma mazauna yankunan da suka tsallake rijiya da baya sun ce kimanin mutane 200 ne suka mutu a harin da aka kai kananan hukumomin Bukkuyum da Anka da ke jihar.
Asali: Legit.ng