Turawan Mulkin Mallaka Suka Ƙirƙiri Bikin New Year, MURIC Ta Ce Buhari Ya Dena Bada Hutun Ranar 1st January
- Kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC ta bukaci gwamnatin tarayya ta yi gyara a kan hutun sabuwar shekara, ta mayar da ranar 1 ga watan Muharram hutu kamar yadda 1 ga watan Janairun ko wacce shekara ya ke hutu
- Kamar yadda darektan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya fadi a wata takarda da ya saki, ya ce hutun sabuwar shekarar kiristoci da ake bayarwa ba adalci ba ne ga musulmai saboda ba a bayar da hutun a duk watan Muharram
- Don haka ya zargi shugaban kasa Buhari da goyon bayan mayar da Najeriya kasar kiristoci da kuma ba shagulgulansu muhimmanci fiye da na musulmai
Kungiyar kare hakkin musulmai, MURIC ta bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi gyara a kan hutun da ta ke bayarwa, ta mayar da daya ga watan Muharram na shekarar musulunci a matsayin ranar hutu, NewsWireNGR ta ruwaito.
Kungiyar ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da bayar da hadin-kai wurin mayar da Najeriya kasar kiristoci inda ake kyale bukukuwan musulunci a bayar da hutu a lokacin na kiristoci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda takardar wacce darektan MURIC ya saki, Farfesa Ishaq Akintola, ya saki, kungiyar ta zargi yin shagulgulan bikin sabuwar shekarar kiristoci a matsayin rashin adalci ga musulman Najeriya kuma hakan bai yi daidai da demokradiyya ba.
Ya kamata a dinga bayar da hutu a farkon shekarar musulunci
NewsWireNGR ta yanko wani bangare na takardar, inda darektan ya ke cewa:
“Kamar yadda mu ka sani, gwamnatin tarayya ta sa ranar 1 ga watan Janairun 2022, a matsayin ranar hutu wacce hakan ta zo daidai da ranar farko ga kalandar sabuwar shekarar kiristoci.
“Hakan yana nuna cewa gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta na bin bayan mayar da Najeriya kasar kiristoci. Ana girmama farkon kalandar kiristoci yayin da ba a ko kulawa da ranar farko ta kalandar musulmai.”
MURIC ta nuna rashin jin dadinta a kan wannan shirin. Babu adalci a cikinsa kuma ba haka demokradiyya ta ce ba. Mu na bukatar gwamnatin tarayya ta yi gyara a kan hutun.
“Mu na bukatar gwamnatin tarayya ta mayar da ranar farko ta watan Muharram na kalandar musulunci a matsayin hutu kamar yadda ranar daya ga watan Janairu ko wacce shekarar kiristoci ta zama ranar hutu a ko wacce shekara."
MURIC ta ce matsawar gwamnatin tarayya ta ki yin wannan daidaiton bayar da hutu a na musulunci, ya kamata ta daina bayar da hutu ranar farko ga watan farko na shekarar kiristoci.
Rashin adalci ne kin daidaita addinan biyu
A cewar Akintola cutarwa ne ga musulmai a ki sa ranar daya da watan farkon ko wacce shekarar musulunci a matsayin hutu.
Ya kara da cewa shekaru 62 kenan da Najeriya ta samu ‘yancin kanta kuma tsawon shekarun ana shagalin ranar farkon shekarar kiristoci.
Hakan rashin adalci ne da nuna fifiko ga kiristoci inji Akintola. Kuma a cewarsa, matsawar ba za a koma ana hutu a ranakun da demokradiyya ta tanadar ba kadai, ba a yi adalci ba.
Ya ce bai dace gwamnatin tarayya ta dinga ba wani bangare fifiko ba fiye da dayan, ya kamata ta kawo daidaito a tsakani.
Idan aka daidaita aka mayar da ranar 1 ga watan Muharram a matsayin hutu, za mu ji dadi kuma mu san cewa ba cutar da mu ake yi ba, a cewar Akintola.
Yadda na yi garkuwa da kwastoma na da taimakon jami’an DSS 5, cewar Ogunnibi mai shekaru 42
Ba Zata Saɓu Ba: Ba Za Mu Amince Da Haramtawa Mata Musulmi Saka Niqabi Ba a FUNAAB, In Ji MURIC
A wani labarin, kungiyar ta MURIC ta nuna rashin amincewarta da hana sa niqabi ga matan musulmai da hukumar Jami’ar Noma ta Tarayya da ke Abeokuta, FUNAAB ta yi, Daily Nigerian ta ruwaito.
Jami’an tsaron makarantar sun tilasta wa wata mata wacce ta kammala jami’ar cire niqabin da ke sanye a fuskarta sannan su bar ta ta shiga makarantar.
Yayin mayar da martani akan wannan lamari, darektan MURIC, Ishaq Akintola, a wata takarda ta ranar Lahadi, ya ce kowa ya na da damar yin shigar da addininsa ya yarje masa a duk jami’o’in kasar nan.
Asali: Legit.ng