Gwamnatin Zamfara ta daura alhakin sabon harin jihar kan masu yiwa ‘yan bindiga kwarmato

Gwamnatin Zamfara ta daura alhakin sabon harin jihar kan masu yiwa ‘yan bindiga kwarmato

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta daura alhakin hare-haren da aka kai wasu garuruwan jihar kan masu yiwa ‘yan bindiga kwarmato
  • Kwamishinan labaran jihar, Ibrahim Dosara ya ce masu yiwa mutanen leken asiri kan samar masu bayanai ta yadda da zaran an sauya dabara sai suma su sauya tasu
  • Yawan adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da yan bindiga suka kai kauyukan jihar ya kai 200

Zamfara - Rahotanni sun kawo cewa yawan mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da yan bindiga suka kai kauyukan jihar Zamfara, a farkon makon nan ya tasar ma 200, The Cable ta rahoto.

A cewar jaridar Punch, wadanda suka tsallake rijiya da baya a harin sun ce 'yan bindiga sun kashe mazauna kauyuka su sama da 200 sannan suka kona gidaje da dama.

Kara karanta wannan

Matawalle ya magantu kan sabon harin Zamfara, ya ce za a tura manyan jiragen yaki jihar

Gwamnatin Zamfara ta daura alhakin sabon harin jihar kan masu yiwa ‘yan bindiga kwarmato
Gwamnatin Zamfara ta daura alhakin sabon harin jihar kan masu yiwa ‘yan bindiga kwarmato Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Da yake martani a kan harin, Ibrahim Dosara, kwamishinan labaran jihar Zamfara, ya dora alhakin hare-haren akan masu yiwa 'yan bindiga leken asiri, jaridar The Cable ta rahoto.

Dosara ya ce:

"Daya daga cikin manyan matsalolin da muke fama da shi, shine muna da masu kwarmato da dama da ke yiwa samarwa wadannan mutane bayanai. Da zaran ka shirya dabara, a nan take makiyan ma za su sauya dabara."

A cewar rahoton, kwamishinan ya kuma ce an tura jirgin yakin sojoji tare da rundunonin tsaro domin su bi sahun 'yan bindigar.

Sabon harin Zamfara: Mutane 36 aka kashe a yankin Bukkuyum – Gwamna Matawalle

A gefe guda, mun ji cewa Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana cewa mutane 36 'yan bindiga suka kashe a sabon harin da suka kai karamar hukumar Bukkuyum da ke jihar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake tare babbar hanya a Arewa, sun kashe mutane sun sace wasu 40

A wata hira da yayi da sashin Hausa na BBC, Matawalle ya bayyana cewa ya kai ziyarar gani da ido kananan hukumomin Anka da Bukkuyum domin tabbatar da irin ta'asar da maharan suka yi.

Matawalle ya kuma bayyana cewa yanzu haka suna da sunaye da bayanai na mutanen da suka rasa rayukansu a harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng