Dokar hana babura: 'Yan Kaduna sun kagu a dage dokar hana babura bayan watanni uku

Dokar hana babura: 'Yan Kaduna sun kagu a dage dokar hana babura bayan watanni uku

  • Mazauna jihar Kaduna sun fara nuna farin cikinsu da karewar wa'adin dokar hana zirga-zirgar ababen hawa a jihar
  • A baya gwamnati ta hana baburan kasuwanci a wasu yankunan jihar, lamarin da wasu 'yan jihar suka ce ya ba su wahala
  • A yau dai dokar ta kare, sun kuma magantu kan dokar, inda suka ce suna jiran sanarwar gwamnati na dage dokar

Kaduna - Watanni uku bayan da gwamnatin jihar Kaduna ta haramta amfani da babura a matakan inganta tsaro da dakile barnar ‘yan bindiga, mazauna jihar sun nuna jin dadinsu ganin cewa dokar ta cika wa'adin watanni uku da aka sanya.

An ruwaito cewa har yanzu gwamnatin jihar ba ta sanar da dage dokar ba amma mazauna yankin da suka zanta da Daily Trust a ranar Laraba sun ce suna da yakinin za a dage dokar.

Kara karanta wannan

Hatsarin jirgin ruwa ya halaka magidanci, matansa biyu da dansa a Neja

Taswirar jihar Kaduna: Dokar hana babura a jihar Kaduna
Dokar hana babura: 'Yan Kaduna sun kagu a dage dokar hana babura bayan watanni uku | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A ranar 29 ga watan Satumba ne gwamnatin jihar ta sanar da daukar matakan tsaro da suka hada da dakatar da harkokin sadarwa na tsawon watanni uku a sassan jihar da kuma haramta babura kwata-kwata.

An ba da izinin ci gaba da gudanar da ayyukan a daidaita sahu a cikin jihar tsakanin 6 na safe zuwa 7 na yamma.

Sai dai a ranar 26 ga watan Nuwamba, gwamnatin jihar ta dage haramcin sadarwa a lokacin da matafiya suka kasa kira a kawo musu dauki yayin da ‘yan bindiga ke kai hare-hare a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Da yake zantawa da Daily Trust, Ibrahim Badamasi, ya ce ya ajiye babur dinsa a gida tsawon watanni uku da suka wuce, ya kara da cewa ya kosa gwamnati ta dage haramcin.

Kara karanta wannan

Zulum ga 'yan soshiyal midiya: Ku daina kamanta aiki na da na wasu gwamnoni, cin zarafi ne

A cewarsa:

“Kwamishanan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce dakatarwar za ta dauki tsawon watanni uku kacal, kuma muna fatan zai sanar da dage haramcin a yanzu da watanni uku suka cika.
“Watanni ukun da suka gabata sun wahalar da ni da iyalina saboda wasu lokuta muna tafiya na sa’o’i saboda dokar hana zirga-zirga da kuma karancin motocin haya da a daidaita sahu. Muna fatan gwamnatin jihar ba za ta kara ba.”

Za mu koma aiki ko ba a dage dokar hana babura ba

Shima da yake magana, wani dan kabu-kabu, Yohanna Lyop, ya ce ko an dage haramcin ko ba a dage ba, masu sana’ar kabu-kabu za su koma kan tituna domin gwamnatin jihar ta bayyana cewa haramcin na watanni uku ne kacal.

A cewar Yohanna Lyop:

“Babu bukatar jira ko tsammanin wata sanarwa daga gwamnati. Sun ba mu tabbacin cewa dokar za ta dauki tsawon watanni uku kuma yanzu da ta wuce, hakan na nufin a bar mu mu koma kan tituna."

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro

A bangare guda, Legit.ng Hausa ta tattauna da wani mazaunin Zariya, Aliyu Usman, daya daga cikin yankunan da dokar ta shafa, ya bayyana cewa, dokar hanin dama bata wuce sati biyu a jihar ba, inda yace tuni dama mutane sun koma ayyukansu.

Da yake tsokaci kan yadda dokar taje, Aliyu ya ce:

"Abin da ake, dan sanda idan ya tare ka ya kwace mata mashin sai suce zaka ba da kudi ko kuwa a kai ka kotu, idan ka basu dubu biyar za su baka mashin dinka."

A tun farko, gwamnatin jihar Kaduna ta dakatar cin kasuwan mako-mako da aka saba dashi a wasu sassan jihar bayan duba da nazirin tabarbarewar tsaro a wasu kananan hukumomin jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da lamurran tsaro suke kara ta'azzara a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, musamman a jihar Kaduna inda aka samu sabbin hare-hare da suka hada da farmakar Kwalejin sojoji a makon jiya.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun tura sako ga gwamnatin Buhari kan lamarin 'yan bindiga

Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da sabuwar sanarwar dokar ne dauke da sa hannun kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, wanda Legit.ng Hausa ta samo a yau Litinin 30 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.