Gwamnatin Kaduna ta haramta cin kasuwannin mako-mako a kananan hukumomi biyar

Gwamnatin Kaduna ta haramta cin kasuwannin mako-mako a kananan hukumomi biyar

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da sabuwar sanarwar da take haramta cin kasuwar mako-mako a wasu yankuna
  • Hakazalika an haramta sayar da man fetur a cikin jarkoki a yankunan tare da bayar da gargadi ga jama'a
  • Gwamnati ta bukaci mutanen gari da su yi hakurin bin doka tare da ba da hadin kai ga hukumomin tsaro

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatar cin kasuwan mako-mako da aka saba dashi a wasu sassan jihar bayan duba da nazirin tabarbarewar tsaro a wasu kananan hukumomin jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da lamurran tsaro suke kara ta'azzara a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, musamman a jihar Kaduna inda aka samu sabbin hare-hare da suka hada da farmakar Kwalejin sojoji a makon jiya.

Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da sabuwar sanarwar dokar ne dauke da sa hannun kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, wanda Legit.ng Hausa ta samo a yau Litinin 30 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Kwamishinan 'yan sanda ya ba da umarnin a binciko wadanda suka kashe dan sanata

Gwamnatin Kaduna ta haramta cin kasuwannin mako-mako a kananan hukumomi biyar
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Wani yankin sanarwar na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bayan cikakken nazari kan yanayin tsaro da shawarwarin da hukumomin tsaro suka bayar, Gwamnatin Jihar Kaduna na fatan sanar da dakatar da cin dukkan kasuwannin mako-mako a kananan hukumomin Birnin Gwari, Igabi, Giwa, Chikun da Kajuru nan take."

An haramtawa gidajen mai sayar da fetur a cikin jarkoki

A wani bangare na sabuwar dokar da gwamnatin ta sanar, ta bayyana cewa, ta haramtawa gidajen mai sayar da man fetur ga mutanen da ke zuwa da jarkoki a cikin kananan hukumomi biyar na jihar ta Kaduna da aka ambata a baya.

Aruwan, ya sake bayyanawa a cikin sanarwar cewa:

"Gwamnati ta kuma haramta sayar da man fetur a cikin jarkoki a ciki da wajen harabar gidajen mai a cikin kananan hukumomi biyar da aka lissafa, tare da fara aiki nan take.

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar kwastam sun cafke wata mota dauke da bindiga da harsasai

"An umurci jami’an tsaro da su tabbatar an bi wannan umarni.
"An umurci 'yan kasa da su ba da hadin kai ga gwamnati yayin da ake daukar matakan da suka dace kan ta'addanci da aikata laifuka a fadin jihar."

Doka a Zamfara: Gwamna ya ba da umarnin a harbe masu goyon biyu a babur

Kamar dai a jihar ta Kaduna, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ba da umarnin rufe dukkan kasuwannin mako-mako a jihar a matsayin wani mataki na magance matsalar tabarbarewar tsaro a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa gwamna Matawalle ya sanar da hakan ne bayan ya karbi dalibai 18 da aka yi garkuwa da su a Kwalejin Aikin Gona da Kimiyyar Dabbobi ta Jihar dake garin Bakura.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatin jihar ta hana sayar da man fetur a cikin jarkoki a wani mataki na dakile samar da man ga 'yan bindiga, hakazalika da kuma ba da umarnin harbin masu babur dake goyon biyu.

Kara karanta wannan

Doka a Zamfara: Gwamna ya ba da umarnin a harbe masu goyon biyu a babur

Asali: Legit.ng

Online view pixel