Ba za mu amince a kara bamu kyautar alluran Korona mara kyau ba, inji FG

Ba za mu amince a kara bamu kyautar alluran Korona mara kyau ba, inji FG

  • Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa ta ce Najeriya ba za ta sake karbar allurar rigakafin Korona da suka lalace ba
  • NAFDAC ta ce yanzu haka ana sa ran abokan hulda za su baiwa al’ummar kasar alluran rigakafin da akalla zai kai watanni biyar ko shida
  • Hukumar ta ce allurar rigakafin da ke da gajeren lokacin lalacewa ba za su kara karbuwa a wajen gwamnatin Najeriya ba

Lagos - Yayin da ake ci gaba da kokarin kawar da cutar nan ta Korona a duniya, gwamnatin Najeriya ta sake nanata shirinta na ganin ta kare duk wani dan kasa, ta dauki kwakkwaran matakai.

Darakta-Janar na Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce Najeriya ba za ta kara karbar allurar Korona da suka lalace ba.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Gargaɗi 'Yan Najeriya Kan Shan Haɗe-Haɗen Magungunan Gargajiya

Hukumar NAFDAC ta magantu kan allurar Korona
Ba za mu amince a kara bamu kyautar alluran Korona mara kyau ba, inji FG | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, Adeyeye ya ce hukumar NAFDAC na hada kai da abokan hulda a fadin duniya domin tabbatar da cewa allurar rigakafin da ake shigowa da su kasar nan sun dade kafin su lalace.

Yayin da take magana a Legas a ranar Laraba, 28 ga watan Disamba, Adeyeye ya ce wasu daga cikin alluran rigakafin da gwamnatin tarayya ta lalata a baya suna da kankanin lokacin lalacewa.

Ta ce karancin tsowon lokaci kafin lalacewar allurar ya sa ba za a iya amfani da dukkan gudummawar da abokan huldar kasa da kasa ke bayarwa gaba daya ba.

Adeyeye ya ce:

"Lokacin da kasashen da suka ci gaba suka fara amfani da maganin na tsawon watanni, ba mu samu damar yin amfani da su ba har sai da muka fara karbar gudummawa, ba ta hanyar COVAX kadai ba har ma daga wasu kasashe."

Kara karanta wannan

UN ga kasashen duniya: Ba Korona ce kadai annobar ba, akwai wata, kowa ya shirya

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Shugaban Hukumar NAFDAC ya tabbatar wa ‘yan kasar cewa gaba Najeriya za ta rika karbar alluran rigakafi ne kawai masu wa’adin lalacewa na akalla watanni biyar ko shida.

UN ga kasashen duniya: Ba Korona ce kadai annobar ba, akwai wata, kowa ya shirya

A wani labarin, Shugabancin Majalisar Dinkin Duniya (UN) ya tabbatar da cewa Korona ba ita ce annoba ta karshe da duniya za ta shaida ba a nan gaba.

Da yake magana a ranar shiri tsaf na rigakafin annoba ta duniya, babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya lura cewa har yanzu duniya ba ta koyi darussa na martanin gaggawa ga annoba daga abin da ya faru a Korona ba, in ji jaridar The Guardian.

Guterres a cikin sakon nasa na ranar Litinin, 27 ga Disamba, ya ba da sanarwar cewa ya kamata kasashen duniya su bullo da shirye-shiryen da za su iya magance lamura cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Kwastam ta yi babban kamu, ta kame kwantena makare da tramadol na biliyoyi

Asali: Legit.ng

Online view pixel