Abun sha'awa: Tagwayen Asali za su angwance da tagwayen mata

Abun sha'awa: Tagwayen Asali za su angwance da tagwayen mata

  • Fitattun tagwaye kuma mawaka wadanda ake kira da Tagwayen Asali za su angwance da wasu tagwayen a sabuwar shekara
  • Tagwayen sun wallafa a shafinsu na Instagram inda suka sanar da cewa za a daura aurensu a garin Dutsin-Ma da ke jihar Katsina
  • 'Yan uwan junan sun yi shuhura tun bayan da suka fara waka kuma ta karbu yayin da suke kananan shekaru

Kano - Tagwayen Asali, fitattun tagwaye masu kama daya na arewacin Najeriya, sun shirya tsaf domin angwancewa da wasu tagwayen mata a rana daya.

A wata wallafa da suka yi a shafinsu na Instagram, 'yan uwan junan sun sanar da cewa za a yi daurin aurensu a ranar takwas ga watan Janairun shekara mai zuwa a garin Dutsin-Ma da ke jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Kannywood: Dalilin da yasa muka maida fina-finan Hausa kan Youtube, Ali Nuhu

Abun sha'awa: Tagwayen Asali za su angwance da tagwayen mata
Abun sha'awa: Tagwayen Asali za su angwance da tagwayen mata. Hoto daga @arewafamilyweddings
Asali: Instagram
"Tagwaye za su auri tagwaye a Katsina @Tagwayenasali (Hassan Sani Abubakar and Hussaini Sani Abubakar), Hassana Abdu Bawa da Hussaina Abdu Bawa inda za a daura auren a Dutsin-Ma a jihar Katsina a ranar 8 Janairun 2022," wallafar tace.

Hassana Sani Abubakar da Hussaini Sani Abubakar fitattu ne saboda wakar da suke yi ta Hausa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan uwan biyu 'yan asalin jihar Kano ne wadanda suka fara sana'arsu ta waka a kananan shekaru. Sun fara wakar cike da kwarewa a shekarar 2003.

Bayan fara wakarsu ta farko da kundunsu mai suna 'Gyara Kayan Ka', sun dauka salon wakar gambara.

Tuni Hassan da Hussaini suka shiga cikin jerin fitattun mawakan Hausa da wakokinsu masu dadi.

Tagwayen da suka auri tagwaye sun haifi tagwaye a rana daya

A wani labari na daban, wasu hotuna masu matukar bada mamaki na tagwaye maza da suka yi aure rana daya ya bayyana. Tagwayen sun aura mata tagwaye a rana daya kuma sun haifi tagwaye kowannensu a rana daya.

Kara karanta wannan

Aiki ga mai kare ka: Na san matsalar Mambilla, a ba ni shekara 1 a ga canji inji Sabon Minista

'Yan biyun maza masu kama daya an gano sunayensu Sa'ad da Sa'id kuma an ga hotunansu dauke da jariransu.

A yayin da Legit.ng bata tabbatar da sahihancin labarin da ya bayyana tare da hotunan mazan da 'ya'yansu ba, hotunan sun ci gaba da bai wa jama'a sha'awa.

A hotunan masu matukar bada sha'awa da suka karade shafukan sada zumuntar zamani, sabbin iyayen sun rike kyawawan 'ya'yansu cike da kauna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel