Tagwayen da suka auri tagwaye sun haifi tagwaye a rana daya

Tagwayen da suka auri tagwaye sun haifi tagwaye a rana daya

- Wani hoto da ya karade kafofin sada zumuntar zamani na 'yan biyu na rike da tagwayen da suka haifa a rana daya ya janyo cece-kuce

- An gano cewa sunan tagwayen Sa'ad da Sa'id kuma sun yi aure a rana daya

- Hotunan masu matukar bada mamaki sun bayyana inda kowannensu ke dauke da tagwayensa

Wasu hotuna masu matukar bada mamaki na tagwaye maza da suka yi aure rana daya ya bayyana.

Tagwayen sun aura mata tagwaye a rana daya kuma sun haifi tagwaye kowannensu a rana daya.

'Yan biyun maza masu kama daya an gano sunayensu Sa'ad da Sa'id kuma an ga hotunansu dauke da jariransu.

Tagwayen da suka auri tagwaye sun haifi tagwaye a rana daya
Tagwayen da suka auri tagwaye sun haifi tagwaye a rana daya Hoto: OvieSheikh
Asali: Twitter

A yayin da Legit.ng bata tabbatar da sahihancin labarin da ya bayyana tare da hotunan mazan da 'ya'yansu ba, hotunan sun ci gaba da bai wa jama'a sha'awa.

A hotunan masu matukar bada sha'awa da suka karade shafukan sada zumuntar zamani, sabbin iyayen sun rike kyawawan 'ya'yansu cike da kauna.

An gansu su kansu sanye da kaya iri daya da kuma huluna iri daya.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun damke magidancin da yayi wa diyar matarsa fyade

A hoton, dukkan tagwayen na zaune rike da tagwayen inda aka saka musu kaya iri daya.

Legit.ng ta ci karo da kyawawan hotunan ne bayan da wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai suna Oviesheikh ya wallafa hotunan a shafinsa.

Ya wallafa a shafinsa: "Tagwayen da suka auri tagwaye sun haifi tagwaye a rana daya."

A wani labari na daban, wata irin soyayya mai rikitarwa ta ratsa wasu iyalai a kasar Rasha. Tsohuwa mai shekaru 75 ce ake zargi da kwace saurayin diyarta bayan diyar ya ci amanarsa.

Mahaifiyar da diyar sun yi mugun fada mai cike da al'ajabi saboda saurayin. Shi kuwa babu kakkautawa ya koma wurin tsohuwar mai shekaru 75.

Matar mai suna Galina Zhukovskaya tana zama a St Petersburg a yankin yammacin Rasha na Leningrad Oblast. Ta aure tsohon mijin diyarta a 2010 bayan sun kulla alaka sakamakon cin amanarsa da diyarta take yi.

A lokacin da diyarta ta rabu da mijin nata, ta bai wa mijin matsuguni a gidanta wanda daga hakan soyayya ta kullu har suka yi aure.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel