Katsina: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 7 tare da garkuwa da wasu da dama a wasu kauyuka

Katsina: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 7 tare da garkuwa da wasu da dama a wasu kauyuka

  • Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki wasu kauyuku biyu da ke karkashin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina inda su ka halaka a kalla mutane bakwai
  • Mazauna yankunan sun bayyana yadda ‘yan bindigan su ka afka kauyen Unguwar Ibrahim Maiwada da Kanon Haki inda bayan kisan sun yi garkuwa da wasu mazaunan
  • Tun misalin karfe 9 na dare su ka fara kai farmakin har zuwa safiya, sannan su ka zarce Kanon Haki da ke kan babban titin Zaria zuwa Sokoto kamar yadda majiyoyi su ka tabbatar

Katsina - Wasu ‘yan bindiga sun afka kauyuku biyu da ke karkashin karamar hukumar Faskari a jihar, inda su ka halaka a kalla mutane bakwai sannan su ka yi garkuwa da wasu da dama, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu 'yan kasuwa sama da 70 a jihar Kaduna

Wani dan asalin yankin, Lawal Mamman, wanda mazaunin garin Katsina ne ya sanar da cewa sun kai harin ne da misalin karfe 9 na dare.

'Yan bindiga sun kai hari kauyukan Katsina, sun kashe 7 sun sace wasu mata 5
Katsina: Yan bindiga sun kai hari kauyukan Katsina, sun kashe 7 sun sace wasu da dama. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

A cewarsa lamarin ya auku ne a kauyen Unguwar Ibrahim

Maiwada da Kanon Haki, kamar yadda ya shaida ta wayar salula:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Sun kai farmakin tun karfe 9 na dare har zuwa washe gari da safe a Unguwar Ibrahim Maiwada kafin su zarce Kanon Haki da ke kan titin Zaria zuwa Sokoto. Dan uwana ya shaida min yadda ya ga gawawwaki da dama a Kanon Haki yayin da wasu mutanen su ka raunana.”

Ana zargin sun halaka ‘Yan Sa Kan da su ka je mayar musu da harin

Ya shaida yadda ba a san inda ‘Yan Sa Kai shida da su ka yi kokarin mayar da farmakin ‘yan bindigan su ke ba. Amma akwai mazaunan da suke zargin ‘yan bindigan sun halaka su.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mata masu juna biyu sun haihu a kan tsaunuka garin gujewa'yan bindiga

Wani mazaunin Unguwar Ibrahim Maiwada ya shaida wa Premium Times cewa mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon harin.

Kamar yadda ya shaida:

“Abinda muke kyautata zato bisa yadda ‘Yan Sa Kan da su ka bi su suka shaida mana, sun raba kawunansu gida biyu, wasu sun koma Kanon Haki don kai farmaki ne, yayin da sauran su ka wuce daji da mata biyar din da suka sace.”

An yi kokarin tuntubar Kakakin rundunar ‘yan sanda amma abin ya ci tura

Premium Times ta bayyana yadda ta yi kokarin tuntubar Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar don jin ta bakinsa amma abin ya ci tura.

Bai bayar da amsar sakon da aka tura masa ba kuma bai amsa kiran da aka masa ba.

Dama ‘yan bindiga sun saba kai farmaki makamancin hakan a jihar Katsina. Akwai jihohi kamar Zamfara, Sokoto, Kaduna da Neja da suke fama da irin wadannan farmakin.

Kara karanta wannan

Jama’a Sun Shiga Tashin Hankali Bayan Ƴan Bindiga Sun Fatattaki Manoma Daga Gonakinsu, Sun Kuma Sace 2 a Abuja

Su na ci gaba da kai farmakin duk da yadda ake kara tura jami’an tsaro yankunan.

'Yan Bindiga Sun Kai Wa Matafiya Hari, Sun Sace Da Dama a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace matafiya da dama a kan hanyar Kaduna - Birnin Gwari a ranar Laraba bayan kai musu hari kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A halin yanzu ba a samu cikakken bayani ba kan harin da aka kai misalin karfe 11 amma an gano cewa mafi yawancin wadanda abin ya faru da su yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa Kano.

Wani shugaban al'umma, Muhammadu Umaru, ya shaida wa Daily Trust cewa hudu daga cikin makwabtansa suna daga cikin wadanda aka sace, ya kara da cewa yan sanda sun yi wa motoccin da suka kai 20 rakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164