Yadda wani mutum ya rasa ransa wurin satar wayoyin transifoma a Gombe
- Wani mutum ya rasa ransa yayin satar wayoyin transifoma da safiyar Alhamis a Labour Quarters da ke anguwar Tumfure karkashin karamar hukumar Akko da ke jihar Gombe
- Dr Adakole Elijah, shugaban bangaren yada labarai na kamfanin raba wutar lantarki ta Jos (JEDC) ya tabbatar da mutuwar mutumin ga manema labarai a Gombe
- A cewar Elijah, a ranar 16 ga watan Disamba da misalin karfe 3:30 na asuba barawon ya lallaba don sata daga nan ya rasa ransa, duk da dai har yanzu ba a gano sunansa ba
Gombe - Wani mutum ya rasa ransa yayin kokarin satar wayoyin transifoma da sanyin safiyar Alhamis a Labour Quarters da ke garin Tunfure a karamar hukumar Akko cikin jihar, The Nation ta ruwaito.
Dr Adakole Elijah, shugaban bangaren yada labarai na kamfanin rarraba wutar lantarki na Jos (JEDC) ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilin NAN a Gombe ranar Alhamis, Vanguard ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Elijah ya ce:
“A ranar 16 ga watan Disamba da misalin karfe 3:30 na asuba, wani barawo ya rasu yayin da ya ke satar wayoyin transifoma din Labour 1 da ke Tumfure.
“Mutumin ya so sace wayar kebur din da ke saman transiforma din ne.”
‘Yan sanda aka kai wa rahoton mutuwar mutumin
A cewarsa an kai wa ofishin ‘yan sanda da ke Tumfure rahoto daga nan ‘yan sandan su ka dauko gawarsa wanda har yanzu ba a gane ko wanene shi ba.
Ya bukaci mazauna yankuna da su kasance masu kula sannan su dinga kai rahoto akan duk wani lamarin sata, yayin da ya ja kunnen masu barna akan kiyaye yin hakan saboda hatsarin da ke gabansu.
Elijah ya ce JEDC ta fara sa fitillu masu amfani da hasken rana kusa da transfomomi don haske ya hana masu barna aiwatar da hakan.
Wani mazaunin yankin ya ce wayoyin wuta barayi ke sacewa
Wani mazaunin yankin, Zakari John ya sanar da NAN cewa wannan ba shi ne karo na farko ba da irin hakan ya faru, kuma faruwar hakan na janyo a dakatar da kai wuta a anguwanni.
John ya bayyana yadda su ka taba yin kwana biyar lokacin da aka lalata transformer din anguwarsu wanda ya ja sai da su ka hada kudi kafin su gyara. “Wayoyi dama su ke sata,” a cewarsa.
Ya roki JEDC akan samar da fitillu masu amfani da rana kusa da transformomi don mutanen anguwanni su dinga lura da abubuwan da ke aukuwa kusa da su.
Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Sojan Bogi, Zailani-Ibrahim Da Ya Ƙware Wurin Tatsar Masu Keke Napep
A wani labarin daban, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar damkar sojan bogi wanda ya kware wurin damfarar masu Napep, The Nation ta ruwaito.
Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abdullahi Kiyawa ne ya tabbatar da kamen a wata takarda wacce ya ba manema labarai ranar Talata a Kano.
A cewarsa, wanda ake zargin, Abubakar Zailani-Ibrahim, mai shekaru 27 ya gabatar wa da ‘yan sandan ofishin Rijiyar Zaki kansa a matsayin soja kuma ya je da wani mai Napep.
Asali: Legit.ng