Rahoto: Dalla-dalla kisan mutane 3,125, da sace 2,703 a cikin watanni 11 a Arewa
- Rahoto ya ce an kashe kusan ‘yan Najeriya 3,125 da ba su ji ba ba su gani ba, ta dalilin wasu 'yan ta'adda a arewacin kasar nan
- A gaba kuwa, rahoton ya bayyana cewa an yi garkuwa da ‘yan Najeriya kimanin 2,703 da ba su ji ba ba su gani ba
- Jihohin da suka fi fama da matsalar rashin tsaro sun hada da Kaduna, Zamfara, Sokoto, Katsina, Neja da Borno
Najeriya - A wani abin da zai ci gaba da ba wa ‘yan Najeriya bakin ciki, wani rahoto ya nuna cewa akalla mutane 3,125 ne ‘yan bindiga suka kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba, tare da yin garkuwa da 2,703 a arewacin Najeriya a cikin watanni 11 da suka wuce.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an samu wadannan alkaluman ne daga wani shiri na hukumar kula da harkokin kasashen waje ta Amurka mai suna Nigeria Security Tracker.
Ya kuma kara da cewa rahoton yace an tattaro daga rahoton kwata-kwata da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar daga watan Janairu zuwa Satumba.
Jihohin da lamarin ya fi shafa sun hada da Kaduna, Zamfara, Sokoto, Katsina, Neja da Borno.
Rahoton ya ce wasu alkaluman da gwamnatin Kaduna ta fitar sun nuna cewa akalla mutane 888 aka kashe tare da yin garkuwa da wasu 2,553 a jihar tsakanin watan Janairu zuwa Satumban 2021.
Dalla-dalla: Barnar 'yan bindiga a 2021
A kasa mun tattaro irin barnar da 'yan bindiga suka yi a kowanne wata a 2021:
Janairu - (sassa daban-daban a Arewa) – An kashe mutane 256 tare da sace 309 duk dai daga ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da kuma makiyaya.
Fabrairu - (Zamfara kadai) an kashe 338 tare da sace 489 ciki har da 'yan makaranta 317 na Jangebe.
Maris - (Yankin Arewa) an kashe mutane 308 yayin da aka yi garkuwa da 510. Wadanda aka sace sun hada da dalibai 39 a Kaduna da kuma masu hakar ma’adinai 100 a jihar Zamfara.
Afrilu - (Yankin Arewa) an yi asarar rayuka 371 da ba su ji ba ba su gani ba, yayin da aka sace 296 ciki har da dalibai 23 na Jami’ar Greenfield ta Kaduna.
Mayu - (Yankin Arewa) mutane 404 ne ‘yan bindiga suka kashe wadanda 100 daga ciki aka kashe a jihar Benue kadai. Adadin wadanda aka sace a watan a Arewa kadai ya kai 317 ciki har da daliban makarantar jihar Neja 208 da musulmi 40 yayin da suke sallah.
Yuni - (Yankin Arewa) an ba da rahoton sace mutane 201 yayin da aka kashe mutane 432.
Yuli - An kashe mutane 243 da karin 164 da aka kashe.
Agusta – An cire rahoton kashe mutane 215 yayin da aka yi garkuwa da 169.
Satumba - An samu rahoton sace mutane 54 da kuma kashe 148 a watan Satumba.
Oktoba - An kashe mutane 220 a watan Oktoba yayin da aka sace 64.
Nuwamba - An yi garkuwa da mutum 41 tare da asarar rayuka 148 da ba su ji ba ba su gani ba.
Disamba - (har yanzu ana ci gaba da kirge tunda watan bata kare ba) akalla an kashe mutum 42 yayin da aka sace 89 a watan Disamban nan.
Duk da haka, ya kamata a lura cewa alkalumman da ke sama na iya bambanta da ainihin alkaluman sace-sace da kashe-kashe saboda wasu kashe-kashen da sace-sacen ba a ba da rahotonsu ba.
Rahoto: Kudurorin gwamnatin Buhari da zasu jefa 'yan Najeriya cikin bakaken wahalhalu a 2022
Bayan karewar 2021, ’yan Najeriya na shirin shiga tsaka mai wuya a shekarar 2022, shekarar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke gab da barin Aso Rock.
Yayin da gwamnatin Buhari ke neman karin kudaden shiga domin biyan basussukan da ke kara yawa, za ta kwakule aljihun ‘yan Najeriya a shekara mai zuwa.
Gwamnati ta ci gaba da kokawa da cewa tana da karancin albarkatun kasa don bi da yawan jama'a da ke kara yawa a kasar.
Asali: Legit.ng