Dama Na San Babu Wani Abin Arziki Da Gwamnatin Buhari Za Ta Tsinana Wa Najeriya, Fasto Oyedepo

Dama Na San Babu Wani Abin Arziki Da Gwamnatin Buhari Za Ta Tsinana Wa Najeriya, Fasto Oyedepo

  • Babban fasto mai cocin Living Faith Church Worldwide, Bishop David Oyedepo, ya ce tun farko dama ya san gwamnatin Muhammadu Buhari ba za ta yi wa Najeriya wani abin kirki bane
  • Oyedepo ya yi wannan furucin ne a wani shiri na Shiloh, inda ya ce bai damu da halin rashin tsaro da lalacewar tattalin arzikin da kasar nan take fama da shi ba
  • A cewarsa dama ya ja kunnen ‘yan Najeriya akan gwamnatin nan don ta fi ko wacce gwamnati lalacewa da tabarbarewa amma su ka yi kunnen uwar shegu da shi

Fasto kuma mai cocin Living Faith Worldwide, Bishop David Oyedepo, ya ce tun farko ya san gwamnatin Muhammadu Buhari ba za ta wani tabuka wa Najeriya komai ba, NewsWireNGR ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba Kayan Matan Jaruma Ne Ya Raba Aure Na da Laila Ba, Baƙin Halinta Ne – Biloniya, Ned Nwoko

Yayin jawabi a wani shiri na Shiloh, ya ce bai damu da halin rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin da kasar nan ta ke fama da su ba.

Dama Na San Babu Wani Abin Arziki Da Gwamnatin Buhari Za Ta Tsinana Wa Najeriya, Fasto Oyedepo
Na San Babu Wani Abinda Gwamnatin Buhari Za Ta Tsinana Wa Najeriya, Fasto Oyedepo. Hoto: The Nation

Ya ce dama ya ja kunnen ‘yan Najeriya

A cewarsa dama ya ja kunnen ‘yan Najeriya akan wannan gwamnatin amma su ka yi kunnen uwar shegu da shi.

Ya kara da cewa wannan gwamnatin ita ce wacce ta fi ko wacce lalacewa a tarihin gaba daya kasar nan.

Matsalolin Najeriya ba su hana shi bacci ba

Kamar yadda ya shaida:

“Ban taba hana kaina bacci ba akan matsalolin kasar nan amma abinda Ubangiji ya sanar da ni, ina fadin shi a bayyane ba tare da jin kunya ko tsoro ba. Kullum cikin kwanciyar hankali na ke.

Kara karanta wannan

Ba dalilin da zai sa APC ta sha ƙasa a zaben 2023 domin yan Najeriya na jin dadin mulkin Buhari, Gwamna

“Na san babu wani abin kirki da gwamnatin nan za ta tsinana wa kasar nan tun farko.
“Wannan gwamnatin ce mafi munin gwamnati da ta taba mulkar kasar nan cike da zalunci. Babu inda ba ta lalata ba. Amma dama na fadi, na kara fadi, kuma ban taba musantawa ba.”

Rashin Adalci Ne Musulmi Ya Zama Shugaban Ƙasa Bayan Buhari, Ƙungiyar Kirista, PFN

A baya, Kungiyar Kirista ta Pentecostal Fellowship of Nigeria, PFN, ta bukaci cewa kirista ne ya dace ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023, tana mai cewa rashin adalci ne wani musulmi ya sake zama shugaba.

Shugaban PFN na kasa, Bishop Francis Wale-Oke, ne ya yi wannan kiran a karshen taron kungiyar da aka saba yi duk bayan wata hudu, da wannan karon aka yi a Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel