Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da babbaka matafiya 42 da akayi a Sokoto

Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da babbaka matafiya 42 da akayi a Sokoto

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alhinin kisan gillan da aka yiwa matafiya a jihar Sokoto.

A jawabin da ya saki ranar Laraba a shafinsa na Facebook, Shugaban kasan ya yi Alla-wadai da irin kisan zaluncin da aka yiwa wadannan fasinjoji ba gaira ba dalili.

Buhari ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa yan uwansu kuma ya lashi takobin kawo karshen wadannan azzaluman mutane.

Shugaba Buhari yace:

"Ina matukar alhinin yadda aka kashe mutanen a jihar Sokoto da suke tafiyarsu zuwa wani sashen kasar nan."
"Ina aika sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan, kuma ina tabbatar musu da cewa jami'an tsaro zasu cigaba da kokarin kawo karshen hare-haren wadannan azzaluman mutane."

Kara karanta wannan

Uwargida ta waskawa miji mari ana tsakiyar shirin ma'aurata a gidan Rediyo, bidiyo

Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da babbaka matafiya 42 da akayi a Sokoto
Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da babbaka matafiya 42 da akayi a Sokoto
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng